Jihohi 3 da Tun Daga 1999 Zuwa 2024, Har Yanzu PDP ba ta Taba Yin Gwamna ba
A shekarar 1999 aka dawo mulkin farar hula a Najeriya, akwai jihohin da duk tsawon shekarun nan, jam’iyya daya ta ke mulki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
A rahoton nan, Legit Hausa ta tattaro jerin jihohin da har zuwa yau, jam’iyyar PDP ba ta taba lashe zaben gwamna, ta yi mulki ba.
Jihohin da PDP ba ta taba mulki ba
1. Yobe
Duk irin karfin da jam’iyyar PDP ta yi a Najeriya, ko da wasa ba ta taba samun nasara a zaben gwamna da aka yi a jihar Yobe ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A duka zabukan da aka shirya a 1999, 2003, 2007, 2011, 2015, 2019 da 2023, jam’iyyun APP, ANPP da APC ne kurum suke nasara.
Gwamnonin da suka yi mulki karkashin jam’iyyun nan su ne: Bukar Abba Ibrahim, Mamman Ali, Ibahim Gaidam sai Mai Mala Buni.
2. Borno
PDP ba ta taba shishina kamshin mulki a Borno mai makwabtaka da jihar Yobe ba. Borno tana cikin wurare da PDP ba ta da tasiri.
Ko a lokacin da jam’iyyar PDP take rike da mulkin tarayyar Najeriya, sai dai ta ga APP da ANPP suna mulki, daga baya aka kafa APC.
Abubakar Mala Kachalla da Ali Modu Shariff sun yi mulki a jam’iyyun hamayya sai Kashim Shettima da Babagana Zulum a jam’iyya mai-ci.
3. Legas
A zabukan 2003, PDP ta yi nasarar karbe duka jihohin Kudu maso yamma daga hannun ‘yan adawa illa Legas a lokacin Bola Tinubu.
Legas ita ce jihar da ta fi kowace arziki a Najeriya, amma haka jam’iyya mai mulki tsakanin PDP ta bar ta kuma ta kyale na shekaru 16.
Bayan Bola Tinubu, ana zargin shi ya jawo Babatunde Fashola, Akinwumi Ambode sai kuma yanzu Babajide Sanwo Olu yana mulki.
Jam'iyyar PDP da jihar Zamfara
Zamfara tana cikin jihohin da PDP ba ta taba cin zaben gwamna ba, amma ta yi mulki har sau biyu a shekarar 2008 da kuma 2019.
Mahmud Aliyu Shinkafi ya koma PDP bayan lashe zabe a APC, sannan Bello Matawalle ya zama gwamna da aka soke nasarar APC.
Dakatar da Sanatan PDP a majalisar dattawa
Kuna da labari cewa ana ji ana gani aka dakatar da Abdul Ahmed Ningi daga majalisar dattawa saboda yunkurin kare Arewa.
Shugaban Arewa Defence League ya ce bai dace Sanatocin Arewa su bari a rufe bakin Abdul Ningi mai wakiltar Bauchi ta tsakiya ba.
Asali: Legit.ng