Rikicin Gida: Matashi Ya Bar PDP Saboda Gaza Ladabtar da Mutum 2 da 'Suka Ci Amana'

Rikicin Gida: Matashi Ya Bar PDP Saboda Gaza Ladabtar da Mutum 2 da 'Suka Ci Amana'

  • Aliyu Abubakar Tanimu Kwarbai ya jefar da katinsa na zama ‘dan jam’iyya ana tsakiyar fama da 'yan sabani a PDP
  • Matashin ‘dan siyasar ya yi alkawari dama zai rabu da jam’iyyar adawar muddin aka ki ladabtar da wasu ‘yan siyasa
  • Kwarbai ya fadawa Legit Hausa cewa ya aikawa shugaban PDP na mazabarsa a Zariya wasika cewa ya bar jam’iyyar

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna – Aliyu Abubakar Kwarbai matashi ne wanda yake cikin magoya bayan jam’iyyar PDP a garin Zariya a jihar Kaduna.

Legit Hausa ta zanta da Aliyu Kwarbai a yammacin ranar Asabar, inda ya tabbatar mata da cewa ya yi ban-kwana da PDP.

Ya bar PDP
Aliyu Kwarbai ya bar PDP a Kaduna saboda rikicin jam'iyya Hoto: @AliyuKwarbai, Getty Images
Asali: Twitter

Aliyu Kwarbai ya fusata da lamarin PDP

Kara karanta wannan

Kwankwaso da 'yan Kwankwasiyya sun ci amanata, wanda ya kafa NNPP ya fame tsohon 'yambo

Dama can Malam Aliyu Kwarbai ya sanar da jam’iyyar idan aka ki daukar mataki, zai jefar da katinsa na zama 'danta a Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake magana a dandalin X, ‘dan siyasar ya bukaci a kori ko akalla a dakatar da wasu jiga-jigan jam’iyyar masu raba kafa.

Daga cikin wadanda yake so a dauki mataki a kansu har da Namadi Sambo da Nyesom Wike bisa zargin cin amana a 2023.

An so PDP ta kori Wike, Namadi

"Idan @OfficialPDPNig ba ta dakatar ko kori Nyesom Wike ko Namadi Sambo nan da mako guda ba, zan mika katin zama ‘dan jam’iyyata ga shugaban mazabata."
"Sannan zan umarci magoya bayana, abokai, da abokan aiki da suyi haka. Mun sadaukar da ranmu sosai, ba za a cigaba a haka. Mashiryamaciyar jam’iyyar adawa."

- Aliyu Kwarbai

Kara karanta wannan

Jihohi 5 da mulkinsu bai taba barin hannun jam’iyyar PDP ba a tsawon shekara 25

...matashin ya sanar da barin jam'iyyar PDP

Wasikar da aka aika a ranar Juma’a ta tabbatar da ya yi murabus bayan shekaru takwas yana goyon bayan PDP a Zariya.

Kwarbai ya fadawa Legit cewa ba za su cigaba da kallon wadanda suke yi wa APC aiki suna halartar taron jam’iyyar PDP ba.

Matashin ya kawo misalin Samuel Ortom wanda ake damawa da shi duk da ya ce zai goyi bayan Bola Ahmed Tinubu ne a 2027.

Jam'iyyar PDP da siyasar jihar Kaduna

A siyasar Kaduna, ya yi ikirarin tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo suna cin dunduniyar jam’iyyar PDP a gida.

Muddin PDP ba ta hukunta su ba, Kwarbai ya ce za a birne PDP a siyasar Kaduna.

Jihohin da PDP take mulki tun 1999

Daga 1999 har zuwa yau, akwai jihohin da har gobe PDP ce ta ke rike da su a matakin gwamna kamar yadda aka kawo rahoto.

Kara karanta wannan

Taron NEC: Babban jigo ya buƙaci shugaban PDP na ƙasa ya yi murabus nan take

Jam'iyyar PDP ta yi tashe musamman saboda yin shekaru 16 a jere tana kan karagar mulki, amma a yanzu APC ce ke da iko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel