Bello Matawalle: Wanda ya fadi zabe amma zai zama Gwamna

Bello Matawalle: Wanda ya fadi zabe amma zai zama Gwamna

A yau mun kawo maku takaitaccen tarihin rayuwar ‘Dan takarar jam’iyyar PDP na Gwamna a Zamfara a zaben da ya gabata watau Dr. Bello Mutawalle wanda ke shirin karbar mulkin jihar a makon nan.

1. Haihuwa

Bello Matawalle zai shiga cikin sahun Gwamnoni masu kananan shekaru a Ranar Laraba idan aka rantsar da shi. An haifi Matawalle ne a Disamban 1949 a cikin Garin Muradun. A karshen shekarar nan ne zai cika shekara 50 a Duniya.

2. Karatu

Matawallen Muradun ya soma karatunsa ne a gida watau cikin karamar hukumar Muradun inda yayi firamare ya kare a 1979. Bello Matawalle yayi karatu a kwalejin fasaha ta Yaba da ke Legas sannan kuma ya tafi wata Jami’a a Landan.

3. Aikin Gwamnati

Mai shirin zama Gwamnan na Zamfara yayi aikin malanta a makarantun gwamnatin jihar Sokoto da ke Garin Moriki da Kwatarkwashi a karkashin ma’aikatar lafiya. Daga baya kuma ya koma Ma’aikatar harkar ruwa ta tarayya.

KU KARANTA: Jerin 'Yan takarar PDP da su ka samu mulki a sama a Zamfara

Bello Matawalle: Wanda ya fadi zabe amma zai zama Gwamna

Matawallen Muradun yayi karatu a Jami’ar Thames Valley da ke Ingila
Source: Facebook

4. Siyasa

A 1998 ne Mutawallen Muradun ya shiga harkar siyasa, ya zama ‘dan jam’iyyar UNCP. Bayan kafa gwamnatin ANPP a Zamfara ne ya zama Kwamishinan harkar kananan hukumomi, daga baya kuma aka nada sa Kwamishina na Matasa.

5. Takara

A 2003 Mutawallen Muradun ya nemi takarar kujerar majalisar tarayya mai wakiltar Muradun da Bakura. Wannan ya sa ya bar gwamnatin Ahmad Yariman-Bakura. Mutawalle ya tafi majalisar har sau 3 inda ya bar kujerarsa a 2015.

6. Sauya-sheka

Bello Matawalle ya bar jam’iyyar ANPP ne ya koma PDP a 2009 lokacin da aka samu sauyin-siyasa a jihar Zamfara. A karkahsin jam’iyyar PDP ne Matawalle ya sake samu ya koma majalisa a zaben 2011 wanda ya zama karon karshe.

7. Gwamnan Zamfara

A 2019 ne Bello Matawalle ya tsaya takarar Gwamna inda yayi alkawarin maida hankali a kan harkar ilmi da kiwon lafiya da sha’anin tsaro idan ya samu mulki. Ko da ya fadi zabe, kotu ta ba sa nasara bayan kuri’un APC sun tashi a tutar babu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel