Wanene Babajide Sanwo-Olu wanda ke neman zama Gwamnan Legas

Wanene Babajide Sanwo-Olu wanda ke neman zama Gwamnan Legas

Mun tsakuro maku kadan na takaitaccen tarihi game da ‘Dan takarar da ya tika Gwamnan Jihar Legas Akinwumi Ambode da kasa a zaben fitar da gwani na Jam'iyyar APC mai mulki. Wannan dai ba kowa bane sai Babajide-Sanwo Olu.

Babajide Sanwo-Olu shi ne wanda zai rikewa Jam’iyyar APC tutan Jihar Legas a 2019. Ga kadan daga labarin wannan ‘Dan siyasa:

Wanene Babajide Sanwo-Olu wanda ke neman zama Gwamnan Legas
Babajide Sanwo-Olu ne zai yi takarar Gwamnan Legas a APC a 2019
Asali: Twitter

1. Babajide Sanwo-Olu yana da aure da Iyali kuma yana da shekaru 53 ne yanzu a Duniya.

2. Sanwo-Olu babban Ma’aikacin banki ne kafin ya ajiye aikin ya shiga harkar Gwamnati. Sanwo-Olu yayi aiki da irin Bankin Lead Merchant Bank, UBA, da kuma FCMB inda ya rike mukamai barkatai har da Mataimakin Manaja.

3. Sanwo-Olu ya taba rike shugaban kamfanin Baywatch Group Limited na Najeriya.

4. Kafin nan dai Jide Sanwo-Olu yayi karatu ne a Jami’ar Legas inda ya karanta harkar gine-gine. Sanwo-Olu yana da Digiri da kuma Digir-gir a wannan fanni.

5. Daga nan kuma ya zarce zuwa manyan Jami’o’in kasuwancin da ake ji da su a Amurka da kuma Ingila har da Makarantar koyon kasuwanci ta Najeriya watau LBS.

KU KARANTA: Abubuwa 10 da ya kamata ka sani game da sabon Gwamnan Osun

6. A shekarar 2003 ne Mataimakin Gwamnan Legas Femi Pedro ya nada Sanwo-Olu a cikin masu ba shi shawara.

7. Bayan nan kuma Sanwo-Olu ya rike Kwamishinan tsare-tsaren tattali da na kasafin kudi a matsayin rikon-kwarya a Legas.

8. A lokacin da Bola Tinubu zai bar mulki ne kuma ya nada Babajide Sanwo-Olu a matsayin Kwamishinan masana’antu da na kasuwanci.

9. Tsakanin 2007 kuma zuwa 2015, Babajide Sanwo-Olu ya rike Kwamishinan harkar fansho da na horas da Ma'aikata a Gwamnatin Fashola.

10. Yanzu haka Ambode ya jawo Babajide Sanwo-Olu a Gwamnatin sa inda ya nada sa Shugaban Hukumar LSPD ta Jihar.

Babajide Sanwo-Olu dai yayi aiki da Gwamnoni 3 a Legas kuma yana cikin wadanda su kayi namijin kokari wajen hawan Babatunde Fashola da Akinwumi Ambode Gwamna a Legas. Babajide Sanwo-Olu ya samu kyaututtuka a bangarori da dama a rayuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel