Sanatocin Arewa 58 Sun Shiga Uku Saboda Sun Kyale An Dakatar da Ningi a Majalisa

Sanatocin Arewa 58 Sun Shiga Uku Saboda Sun Kyale An Dakatar da Ningi a Majalisa

  • Mutanen Arewacin Najeriya suna da Sanatoci 55 da ke wakiltarsu a majalisar dattawa kamar yadda doka ta yi tanadi
  • Arewa Defence League ta yi tir da yadda wadannan ‘yan siyasa suka zura idanu har aka dakatar da Abdul Ningi a majalisa
  • Kungiyar ta so wakilanta su kare Sanatan na Bauchi wanda shi ne shugaban kungiyar sanatocin jihohin Arewacin kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna - Wata kungiya da aka kafa domin kare muradun mutanen Arewacin Najeriya ta soki sanatocin da suka fito daga yankin.

Arewa Defence League ta yi Allah-wadai da yadda aka dakatar da Abdul Ahmed Ningi daga majalisar dattawa a kwanakin baya.

Abdul Ningi a Majalisa
An dakatar da Abdul Ningi a Majalisar Najeriya Hoto: @NgrSenate, @sen_abdulningi
Asali: Twitter

Kungiya ta ji haushin dakatar da Ningi

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa na shirin ɗage dakatarwan da ta yi wa Sanata Abdul Ningi, ta faɗi dalili

A karshen makon nan Daily Trust ta rahoto Arewa Defence League tana sukar yadda duk Sanatocinta suka ki tsayawa Abdul Ningi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kungiyar Arewa Defence League na kasa, Murtala Abubakar ya bayyana fushinsu da ya zanta da ‘yan jarida a Kaduna.

A matsayin Sanata Abdul Ningi na shugaban sanatocin yankin Arewa a lokacin, Murtala Abubakar ya ce ya kamata a kare shi.

Matsayar Arewa Defence League a kan Ningi

Abubakar yana ganin cewa bai dace ‘yan majalisar da suka fito daga Arewa su kyale a dakatar da abokin aikin nasu daga ofis ba.

Leadership ta ce kungiyar ta bukaci wakilan da aka zaba daga yankin na Arewa su yi kokari wajen magance matsalolin mutanensu.

Arewa Defence League ta ce rashin tsaro ya hana mutane zuwa makarantu da gonaki, amma sanatoci sun manta da mazabunsu.

Kara karanta wannan

Zargin yi wa kasurgumin dan bindiga Dogo Gide magani, asibitin Sokoto ya magantu

Ningi: Kira zuwa ga shugaba Tinubu

Bayan haka, kungiyar ta bukaci Bola Tinubu ya yi koyi da Umaru Yar’adua da Muhammadu Buhari, ya soki cushe a kasafin kudi.

Murtala Abubakar yana ganin idan aka yi wasa da yadda aka dakatar da Ningi, lamarin zai iya jawo matsalar da ba a yi tunani ba.

Yaushe Abdul Ningi zai dawo kujerarsa?

Ana da labari cewa an fahimci majalisar dattawa ta kasa za ta ɗage dakatarwan da ta yi Sanata Abdul Ningi nan ba da jimawa ba.

Godswill Akpabio ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan ya dawo Najeriya daga Switzerland bayan Sanatan ya nuna zai je kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel