Masoyin Atiku Ya Bayyana Dalilinsa na Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC

Masoyin Atiku Ya Bayyana Dalilinsa na Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC

  • Wanda ya kafa PDP New Generation, Abdullahi Audu Mahmood, ya bayyana dalilin da ya sa ya fice daga jam’iyyar
  • Kwanan nan Mahmood ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a Jigawa, inda dubban magoya bayansa suka tarbe shi
  • Mahmood wanda ya kasance mai goyon bayan Atiku, ya tara matasa miliyan biyar a fadin jihohi 36 domin tsohon mataimakin shugaban ƙasan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Jigawa - Wanda ya kafa PDP New Generation kuma jigo a jam’iyyar PDP, Abdullahi Audu Mahmood, ya bayyana dalilin sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

Ƙungiyar PDP New Generation ta Mahmood ta shahara wajen yin haɗin gwiwa da matasan jam’iyyar domin marawa Atiku Abubakar baya, wanda ya zo na biyu a zaɓen da ya gabata.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta bayyana makudan kudaden da aka sace a gwamnatin APC

Masoyin Atiku ya koma APC
Abdullahi Mahmoud ya fadi dalilinsa na yin kaura daga PDP zuwa APC Hoto: Audu Mahmoud
Asali: UGC

PDP New Generation ƙarƙashin jagorancin Mahmood ta haɗa matasa miliyan biyar a faɗin jihohin Najeriya 36 domin marawa takarar Atiku baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mahmood wanda ya fito daga jihar Jigawa ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

A wata tattaunawa ta wayar tarho da Legit.ng a ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, Abdullahi Audu Mahmood ya bayyana cewa ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar PDP ne kawai saboda son ci gaba ɗa yake da shi.

Ba ya da wata ɓaraka da PDP

Ya bayyana cewa ba shi da wata ɓaraka ko kaɗan da shugabannni da jiga-jigan jam'iyyar PDP a matakin shiyya da ƙasa baki ɗaya.

Mahmood ya bayyana cewa ya yanke shawarar shiga jam’iyya mai mulki ne sakamakon kishi da ƙaunarsa ga siyasar talakawa, da yadda ayyukan Gwamna Umar Namadi suka ba shi mamaki.

A kalamansa:

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta zargi gwamnan PDP da salwantar da N144bn, ta kawo hujja

"Na yanke shawarar komawa siyasar cikin gida ne saboda a zaɓen da ya gabata na tsunduma cikin harkokin siyasar ƙasa, ni mai ci gaba ne kuma na yi imani da haɗin kai da ci gaba.
"Duba da irin nasarorin da mai girma Gwamna Umar Namadi ya samu, cikin ƙanƙanin lokaci, ƙa’idojinsa da salon shugabancinsa na daga cikin abubuwan da suka ja hankalina na yi tunanin shiga jam’iyyar APC."

Dangantaka da Atiku

Da aka tambaye shi ko Atiku yana sane da ficewarsa daga PDP, Mahmood ya bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar ba a samunsa tun bayan zaɓen da ya gabata.

Sai dai ya yi nuni da cewa shugabannin jam’iyyar PDP a matakin gunduma da shiyya suna sane da matakin da ya ɗauka, kuma sun yi masa fatan alkhairi.

A kalamansa:

"Tun bayan zaɓe, ba a samun Atiku, kuma babu yadda zan iya tuntuɓarsa, amma shugabannin jam’iyyar PDP da na ke kusa da su, kamar shugaban matasa na ƙasa, suna sane da ficewata."

Kara karanta wannan

Ganduje ya nakasa PDP yayin da masoyin Atiku, jiga-jigai da dubban mambobi suka koma APC a Arewa

Shugaban Ƙaramar Hukuma Ya Koma NNPP

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa a jihar Kano, zai sauya sheƙa zuwa jam'iyyar NNPP.

Hon Lawal Aranposu na jam'iyyar APC ya fito duniya ya bayyana aniyarsa ta komawa jam'iyyar NNPP mai mulki a Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel