Mataimakin Gwamnan PDP Na Dab da Rasa Kujerarsa Yayin da CJ Ya Kafa Kwamitin Mutum 7

Mataimakin Gwamnan PDP Na Dab da Rasa Kujerarsa Yayin da CJ Ya Kafa Kwamitin Mutum 7

  • Batun tsige mataimakin gwamnan jihar Edo ya sake tasowa yayin da babban alƙalin jihar ya bi umarnin majalisar dokoki
  • Mai shari'a D. I. Okungbowa ya kafa kwamitin mutum bakwai da zasu gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake wa mataimakin gwamna, Philip Shaibu
  • Babban alkalin ya bayyana cewa ya kafa kwamitin ne duga da tanadin sashi na 188 (5) na kundin tsarin mulkin Najeriya 1999

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Babban alkalin jihar Edo, mai shari'a Daniel Okungbowa, ya kafa kwamitin mutum 7 da zai binciki zargin da ake yi wa mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu.

A makon da ya wuce ne majalisa dokokin jihar Edo ya umarci babban alkalin ya kafa kwamitin da zai gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi wa Shaibu, Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Malam Nasiru El-Rufa'i ya gana da fitaccen sanatan PDP, hotuna sun bayyana

Mataimakin gwamnan Edo, Philip Shaibu.
Babban Alkalin Edo Ya Kafa Kwamitin da Zai Binciki Mataimakin Gwamna Shaibu Hoto: Rt Hon. Comrade Philip Shaibu
Asali: Facebook

Wannan na ɗaya daga cikin matakan da majalisar ta ɗauka a yunƙurinta na tsige Kwamared Shaibu daga kujerar mataimakin gwamna, kamar yadda Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kafa kwamitin binciken ne ranar Jumu'a a wata sanarwa mai lamba CR/4837 /Vol. I/131, wadda magatakardan babbar kotun jihar Edo, B. O. Osawaru, ya rattaɓa wa hannu.

Jerin waɗanda suka shiga kwamitin

Sanarwan ta bayyana cewa tsohon alƙali, mai shari'a S.A. Omonua (mai ritaya) ne zai jagoranci wannan kwamiti, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Farfesa Violet Aigbokhaebo, Farfesa Boniface Onomion Edegbai, Farfesa Theresa Akpoghome, Oghogho Ayodele Oviasu da kuma Idris Abdulkareen.

A sanarwar, babban magatakardar ya bayyana cewa CJ ya yi amfani da ƙarfin ikon da sashe na 188(5) na kundin tsarin mulkin 1999 ya ba shi wajen kafa kwamitin.

Kara karanta wannan

Badaƙalar N3bn: EFCC ta tara sabbin hujjoji, ta sake gurfanar da tsohon gwamna a kotu

Sanarwan ta ce:

"Muna sanar da al'umma cewa bisa la'akari da sashe na 188(5) na kundin tsarin mulki 1999, babban alƙalin jihar Edo, mai shari'a D. I. Okungbowa, ya kafa kwamitin mutum bakwai.
"Kwamitin zai binciki dukkan zarge-zargen da ke kunshe a sanarwar shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu."

Gwamna Sule ya ɗauki mataki kan mutuwar ɗalibai

A wani rahoton kuma Gwamna Abdullahi Sule ya umarci hukumar jami'ar jihar Nasarawa da jami'an tsaro su yi bincike kan mutuwar ɗalibai 2 a wurin rabon tallafi.

Ɗalibai mata biyu ne aka tabbatar sun mutu a wurin wawason tallafin shinkafa da gwamnatin Nasarawa ta shirya rabawa ɗaliban jami'ar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel