Badaƙalar N3bn: EFCC Ta Tara Sabbin Hujjoji, Ta Sake Gurfanar da Tsohon Gwamna a Kotu

Badaƙalar N3bn: EFCC Ta Tara Sabbin Hujjoji, Ta Sake Gurfanar da Tsohon Gwamna a Kotu

  • Hukumar EFCC ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Benuwai, Gabriel Suswam a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja
  • EFCC ta sake gurfanar da tsohon gwamnan kan zargin satar Naira biliyan 3 na jihar Benuwai, inda take tuhumarsa da aikata laifuffuka 11
  • An ruwaito cewa, Suswam ya hada kai da tsohon kwamishinan kudi na Benuwai wajen sace kudin jihar daga hannun jarin kamfanin Dangote

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

FCT, Abuja - Hukumar EFCC ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Benuwai, Gabriel Suswam a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja akan zargin satar Naira biliyan 3.

EFCC ta sake bude shari'arta da Gabriel Suswam
Tsohon gwamna Benuwai, Gabriel Suswam ya sake gurfana gaban kotu a Abuja. Hoto: Gabriel Suswam
Asali: Twitter

EFCC ta sake gurfanar da Suswam ne a matsayin ƙarin hujjoji kan ƙarar farko da ta shigar a 2020 inda take tuhumarsa da aikata laifuffuka 11.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu ta gurfanar da shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah, Bodejo

Laifuffukan da tsohon gwamna ya aikata

Laifuffukan sun hada da sata, zamba cikin aminci, ba da kwangila ba bisa ƙa'ida ba da kuma safarar kudi, wanda ta haɗa da tsohon kwamishinan kuɗi Omadachi Oklobia a shari'ar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ana zargin Suswam da Oklobia sun karkatar da kudin ne daga hannun jarin Benuwai na kamfanin simintin Dangote.

A watan Nuwamba 2025 ne hukumar EFCC ta gurfanar da Suswam da Oklobia a gaban kotun a karo na biyu, wadanda suka ƙaryata zargin da ake yi masu.

Kotu ta bayar da belin tsohon gwamna

Lauyoyin wadanda ake kara, Adebayo Adedeji (SAN) da Paul Erokoro (SAN) sun nemi a ba da balin wadanda ake karar kamar yadda aka yi masu a baya.

Lauyan hukumar EFCC, Leke Atolagbe bai yi musu akan wannan bukatar ba kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ana sa ran naira za ta mike, CBN ya biya bashin Dala biliyan 7 da Emefiele ya bari

Mai shari'a Peter Lifu ya amince da bukatar bayar da belin tare da ɗage shari'ar zuwa ranar 29 ga watan Afrilu 2024.

Kwara: EFCC ta yi karar tsohon gwamna

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa hukumar EFCC ta yi karar tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfattah Ahmed, bisa zargin satar N10bn a lokacin da yake ofis.

Alhaji AbdulWahab Oba wanda shi ne sakataren yada labaran tsohon gwamnan ya ce EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan zuwa ofishinta amma daga bisani ta tsare shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel