Wata Sabuwa: Malam Nasiru El-Rufa'i Ya Gana da Fitaccen Sanatan PDP, Hotuna Sun Bayyana

Wata Sabuwa: Malam Nasiru El-Rufa'i Ya Gana da Fitaccen Sanatan PDP, Hotuna Sun Bayyana

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, ya kai ziyara gidan Sanata Abdul Ningi, wanda majalisar dattawa ta dakatar kwanan nan
  • Majalisa ta dakatar da Sanata Ningi, mamban jam'iyyar PDP mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya saboda zargin cushe a kasafin kuɗin 2024
  • Ziyarar da El-Rufai ya kai gidan Ningi na daga cikin ziyarce-ziyarcen da tsohon gwamnan ke kai wa manyan ƴan siyasa a baya-bayan nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Malam Nasiru El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna ya kai ziyara ta musamman gidan dakataccen sanatan PDP, Abdul Ningi.

Imran Muhammad, jigon jam'iyyar APC ne ya tabbatar da haka a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.

Kara karanta wannan

Ribadu, FFK zuwa Ningi: El-Rufai ya ruda APC, ya tada kura kwatsam a siyasar Najeriya

Ningi da El-Rufai.
Tsohon gwamnan Kaduna ya je gidan Abdul Ningi Hoto: Imran Muhammad
Asali: Twitter

Idan baku manta ba, majalisar dattawa ta yanke shawarin dakatar da Sanata Ningi, mamban jam'iyyar PDP mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya na tsawon watanni uku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ɗauki wannan matakin ne biyo bayan ikirarin da Ningi ya yi cewa an yi cushen kuɗi N3.7trn a kasafin kuɗin 2024 waɗanda babu cikakken bayani a kansu.

Meyasa majalisa ta dakatar da Ningi?

Jim kaɗan bayan wannan zargi da ya yi, abokan aikinsa sanatoci da fadar shugaban ƙasa suka fara sukar sanatan, inda mafi akasarinsu ke ganin bai kamata mutum kamar Ningi ya yi haka ba.

Duk da wannan suka da yake sha, Sanata Ningi ya musanta ikirarin da aka jingina masa cewa yana zargin an yi kasafin kuɗi guda biyu a ƙasar nan.

Ya yi ƙarin bayani cewa yayin da aka ware N25trn domin gudanar da ayyuka, N3.7trn da yake zargin an cusa ba bu wani taƙamaiman bayanin aikin da za a yi da su.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamnan PDP na dab da rasa kujerarsa yayin da CJ ya kafa kwamitin mutum 7

Godswill Akpabio, shugaban majalisar dattawa ya soki ikirarin Ningi, inda ya nemi kaɗa kuri'ar murya kuma mafi yawan sanatoci suka amince a dakatar da shi na watanni uku.

El-Rufai ya gana da Ningi

A halin yanzu, wannan ziyara da Malam El-Rufai ya kai gidan Sanata Abdul Ningi ta shiga cikin jerin ziyarorin da tsohon gwamnan ya kai kwanan nan.

Daga cikin waɗannan ziyara, tsohon gwamnan ya je hedkwatar jam'iyyar SDP da ke birnin tarayya Abuja, inda ya gana da shugaban jam'iyyar, Shehu Gabam.

Ya kuma ziyarci gidan tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma babban jigon APC, Femi Fani Kayode a Abuja.

Tinubu ya caccaki Abdul Ningi

A wani rahoton kuma Shugaban kasa, Bola Tinubu ya caccaki Sanata Abdul Ningi kan zargin cushe a kasafin kudin shekarar 2024.

Tinubu ya ce duk wadanda ke zargin cushen ya tabbata ba su fahimci ilimin lissafi ba kwata-kwata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel