NYCN Ta Tsoma Baki Kan Yunƙurin Tsige Mataimakin Gwamnan PDP, Ta Faɗi Mafita 1 Tak

NYCN Ta Tsoma Baki Kan Yunƙurin Tsige Mataimakin Gwamnan PDP, Ta Faɗi Mafita 1 Tak

  • Kungiyar NYCN ta yi magana kan ƙishin-kishin ɗin cewa ana shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu
  • A wata sanarwa ranar Talata, ƙungiyar matasan ta roƙi Gwamna Obaseki ya tara masu ruwa da tsaki domin lalubo bakin zaren ta hanyar maslaha
  • NYCN reshen nahiyar Turai ta jaddada cewa ba yanzu ya kamata a sauke Shaibu ba, sulhu ya dace a yi domin tunkarar zaɓen gwamna

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Ƙungiyar matasan Najeriya (NYCN) reshen nahiyar Turai ta jaddada cewa ba yanzu ne lokacin da ya dace a tsige mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ba.

Shaibu dai ya ayyana kansa a matsayin halastaccen ɗan takarar PDP a zaben gwamnan jihar Edo mai zuwa a 2024, lamarin ya haifar da ƴan takara biyu.

Kara karanta wannan

Majalisa za ta tunbuke mataimakin gwamna a karshen mulkin PDP

Gwamna Obaseki da Shaibu.
Edo 2024: Ba Yanzu Ya Kamata a Tsige Mataimakin Gwamna Ba, NYCN Ga Obaseki Hoto: Governor Godwin Obaseki
Asali: Facebook

Sai dai ƙungiyar matasan ta hannun shugaban NYCN na ƙasar Sweden, Kwamared Collins Idahosa, ta gargaɗi Gwamna Godwin Obaseki kan tsige Shaibu, The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NYCN ta roƙi Gwamna Obaseki da sauran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP reshen jihar Edo su rungumi sulhu da zaman lafiya maimakon tsige mataimakin gwamnan.

Me ya kamata PDP ta yi don ɗinke ɓaraka a Edo?

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar Talata, 5 ga watan Maris, 2024, ta ce:

"Ba wannan lokacin ya kamata mu fara magana kan sauke shi ba, ita siyasa wasa ce. Kamata ya yi masu ruwa da tsaki su zauna, su tattauna, su lalubo masala kan kowane batu.
"Jihar Edo na bukatar zaman lafiya a yanzu fiye da kowane lokaci. Muna rokon mai girma gwamna, Godwin Nogheghase Obaseki, da sauran masu ruwa da tsaki su rungumi zaman lafiya.

Kara karanta wannan

UAE ta cire takunkumin hana 'yan Najeriya biza? Fadar shugaban kasa ta fadi gaskiya

"Su bi hanyar maslaha domin warware kowane ƙulli maimakon fara tunanin tsige shi (mataimakin gwamna) domin ba zai haifar da ɗa mai ido ba saboda ba haka mutane ke so ba."

Ƙungiyar ta ƙara da cewa Gwamna Obaseki na da ikon tattara duk wanda ya kamata a matsayinsa na uba a jihar Edo domin warware saɓanin da ake da shi.

NYCN ta kuma bayyana cewa gabanin zaben gwamnan jihar da za a yi a ranar 21 ga Satumba, 2024, akwai bukatar hadin kai musamman a jam'iyyar PDP ta Edo, rahoton Vanguard.

Shugaban INEC ya yi nadama kan zaben 2023?

A wani rahoton kuma Gaskiya ta fito game da raɗe-raɗin cewa shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ya yi nadamar ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen 2023.

Tinubu ya lallasa Atiku Abubakar na PDP da takwaransa na Labour Party, Peter Obi a zaɓen shugaban ƙasa da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel