Gwamna Makinde Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Jam'iyyar PDP Ta Rasa Babbar Jiha a Hannun APC

Gwamna Makinde Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Jam'iyyar PDP Ta Rasa Babbar Jiha a Hannun APC

  • Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ta faɗi zaben gwamnan jihar Ondo a 2020 ne saboda rashin haɗin kai da rarrabuwar kawuna
  • Makinde ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar reshen jihar Ondo da ƴan kwamitin NWC na ƙasa
  • Gwamnan na jihar Oyo ya bayyana cewa, domin samun nasarar zaɓen gwamna mai zuwa a Ondo, sai an fafata wajen samun tikitin takarar jam’iyyar PDP

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Seyi Makinde, gwamnan jihar Oyo, ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ta sha kaye a zaɓen gwamnan jihar Ondo na shekarar 2020 ne, saboda rashin haɗin kai da rarrabuwar kawuna a cikin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

NYCN ta tsoma baki kan yunƙurin tsige mataimakin gwamnan PDP, ta faɗi mafita 1 tak

Marigayi Gwamna Rotimi Akeredolu na jam'iyyar APC ne ya lashe wa'adi na biyu a zaɓen gwamnan jihar na 2020.

Makinde ya fadi dalilin rashin nasarar PDP a zaben Ondo
Gwamna Makinde ya fadi dalilin da ya sa PDP ta yi rashin nasara a hannun marigayi Akeredolu a Ondo Hoto: Rotimi Akeredolu, Seyi Makinde
Asali: Twitter

Yaushe ne zaɓen gwamnan Ondo?

Ku tuna cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta tsara sake gudanar da zaɓen gwamna a jihar Ondo a ranar 16 ga watan Nuwamba, 2024, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar PDP ta shirya gudanar da zaɓen fidda gwani na ɗan takarar gwamnan jihar a ranar Alhamis, 25 ga watan Afirilun 2024.

Jam’iyyar PDP za ta fara siyar da fam na neman takara daga ranakun 17 zuwa 21 ga watan Maris na wannan shekarar.

Makinde yayi jawabi a taron PDP NWC

Gwamna Makinde ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki na jihar Ondo da kuma kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP na ƙasa (NWC) a hedikwatar jam’iyyar, dake a Wadata Plaza, a Abuja a ranar Talata, 5 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP zai ba 'yan adawa mukamai masu gwabi a jiharsa, ya fadi dalili

Makinde ya bayyana cewa jam’iyyar ta samu darussa masu ma’ana daga zaɓen gwamnan jihar Ondo na 2020 inda ya ƙara da cewa shugabanni da ƴaƴan jam’iyyar PDP za su iya haɗa kai wajen yin nasara tare da magance ƙalubalen rashin nasara.

A cewar gwamnan, tikitin takarar gwamna na jam’iyyar PDP ba zai samu cikin sauƙi ga duk wani mai neman tsayawa takara ba, inda ya ƙara da cewa duk masu neman tikitin sai sun fafata da juna domin samun takarar, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.

Matar Akeredolu Ta Caccaki Surukarta

A wani labarin kuma, kun ji cewa Betty Akeredolu, matar tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ta caccaki surukarta kan goyon bayan Gwamna Lucky Aiyedatiwa.

Betty ta caccaki Funke Akeredolu Aruna ne bayan ta fito fili ta nuna goyon bayanta ga gwamnan yayin da ake tunkarar zaɓen gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel