Dalilin ficewa ta daga Kwankwasiyya zuwa Jam’iyyar UPC – ‘Dan takaran Nasarawa

Dalilin ficewa ta daga Kwankwasiyya zuwa Jam’iyyar UPC – ‘Dan takaran Nasarawa

Adnan Mukhtar Adam Tudunwada wani Matashi da ke harin kujerar majalisar dokoki na Yankin Nasarawa a Jihar Kano a karkashin jam’iyyar adawa ta UPC yayi hira da Jaridar nan ta Premium Times game da tafiyar siyasar sa.

Dalilin ficewa ta daga Kwankwasiyya zuwa Jam’iyyar UPC – ‘Dan takaran Nasarawa

Adnan Tudunwada (D) yace an hana sa takara ne saboda shi gwauro ne
Source: Facebook

Malam Adnan mai shekaru 26 yayi watsi da ‘Darikar Kwankwasiyya da jam’iyyar PDP bayan Jagoran Kwankwasiyya watau tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ya hana sa takara a PDP. Wannan ta sa tuni ya fice ya koma UPC.

Tudunwada wanda tun 2011 yake cikin fagen siyasa ya rabu da tafiyar Kwankwasiyyar ne bayan an nemi a dakatar da shi daga takara a 2019 saboda karancin shekarun sa da kuma rashin gogewa har da dalilin cewa yanzu bai da aure.

KU KARANTA: 2019: Jam’iyyun hamayya sun kai karar Buhari gaban Alkali

Wannan ne ya kara tunzura Adnan Tudunwada yayi takarar kujerar majalisar dokoki a Jihar Kano, inda yace ya kuma yi tsari wajen ganin yayi nasara. Adnan yace yana da burin ganin matasa sun shigo cikin siyasar kasar nan tsindum.

Wannan matashi yana cikin wadanda su kayi ta fafutukar ganin an yi na’am da kudirin nan na Not To Young To Run domin ire-iren sa su yi takara. Adnan yace idan ya zama ‘Dan Majalisa zai kawo kudirori da za su taimakawa mutanen sa.

Kwanaki kun ji cewa tsohon Gwamnan na Kano Rabiu Kwankwaso ya fito yayi magana game da dalilin da ya sa ya fice daga Jam’iyyar APC mai mulki ya kuma koma Jam’iyyar sa ta asali watau PDP mai adawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel