Yadda Sarkin Kano Aminu Bayero Ya Saba da Sanusi II a Kan Maganar Dauke Ofisoshin CBN

Yadda Sarkin Kano Aminu Bayero Ya Saba da Sanusi II a Kan Maganar Dauke Ofisoshin CBN

  • Aminu Ado Bayero ya fadawa Remi Tinubu koke-koken da talakawasa su ke yi a kan gwamnatin tarayya
  • Sarkin Kano ya soki dauke FAAN da ofisoshin CBN a lokacin da Mai dakin shugaban kasa ta ziyarci fadarsa
  • Shi kuwa Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II yana goyon bayan matakin da gwamnati mai-ci ta dauka

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya nuna rashin kwanciyar hankalinsa game da dauke wasu ma’aikata a Abuja.

Gwamnatin tarayya ta maida hedikwatar FAAN da wasu ofisoshin bankin CBN zuwa garin Legas, wannan ya jawo surutu a fadin kasar.

Aminu Ado Bayero, Sanusi
CBN: Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II Hoto: @HRHBayero, @MSII_Dynasty, @Cenbank
Asali: Twitter

Legit ta rahoto Aminu Ado Bayero yana bayyana wannan mataki a matsayin abin zargi.

Kara karanta wannan

Fitaccen malami ya yi hasashen sabon farashin naira kan dala, ya ce buhun shinkafa zai kai 90k

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai martaba ya bayyana matsayarsa ne a lokacin da Uwargidar shugaban kasa watau Oluremi Tinubu ta kawo ziyara zuwa Kano.

Sanata Oluremi Tinubu ta kai ziyarar ban girma zuwa fadar Sarkin Kano, a nan Mai martaba ya fada mata halin da talakawa suke ciki.

Kiran Sarki Aminu Bayero ga gwamnati

An fassarawa matar shugaban kasar jawabin Sarki Aminu Ado Bayero, inda ya yi maganar janye ma’aikatan CBN da FAAN daga Abuja.

Mutane da-dama sun zargi gwamnatin Bola Tinubu da nuna kabilanci da yunkurin karya yankin Arewa domin a karfafa jiharsa ta Legas.

Sarki Aminu Ado Bayero ya ce suna ta samun irin wannan korafe-korafe daga al’ummarsa kamar yadda aka fitar da jawabin a X.

Muhammadu Sanusi II ya saba

Mai Martaban ya bukaci gwamnatin tarayya ta fito karara ta fadi gaskiya, kuma tayi wa ’yan Najeriya bayanin da za su gane da kyau.

Kara karanta wannan

EFCC: An daure Mama Boko Haram a kurkuku na shekaru 10 saboda zambar N40m

Wannan ya saba da matsayar magabacinsa, Muhammadu Sanusi II wanda yake ganin an yi daidai a dauke wasu ofisoshin bankin.

Sanusi II wanda ya taba zama gwamnan babban bankin ya nuna akwai bukatar bangarorin su bar Abuja, bai hangen wata manufa.

A jawabinsa, Aminu Ado Bayero ya fadawa Remi Tinubu ya kamata su wayar da kan al’umma domin a fahimci niyyar gwamnatin sosai.

A dawo da Sarki Sanusi II

Ana da labari Alhaji Garba Kore Dawakin Kudu ya ce saboda APC ta ci zabe aka kirkiro masarautu, ya ce kyau yanzu a tsige su.

'Dan siyasar yake cewa a karshe kusa duka Sarakunan da Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro ba su hana NNPP karbe mulkin jihar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel