Sarkin Kano na 14 Ya Goyi Bayan Dauke Wani Sashe Na CBN Daga Abuja Zuwa Legas, Ya Fadi Dalili

Sarkin Kano na 14 Ya Goyi Bayan Dauke Wani Sashe Na CBN Daga Abuja Zuwa Legas, Ya Fadi Dalili

  • Tsohon gwamnan CBN, Sanusi Lamido, ya ce matakin da gwamnati ta dauka na mayar da wani bangare na CBN zuwa Legas ya yi dai dai
  • A cewar Sanusi, babu amfanin a rinka gudanar da ayyukan CBN a Abuja alhalin akwai babban ofishin bankin a Legas wanda zai iya daukar kowa
  • Ya tariyo yadda ya so ya dauki irin wannan matakin a lokacin da ya ke gwamnan CBN, sai dai lokaci bai ba shi damar yin haka ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Sanusi Lamido Sanusi ya goyi bayan mayar da wasu sassan babban bankin kasar daga Abuja zuwa Legas.

Ya ce abu ne da ya dace a yi, inda ya yi watsi da masu adawa da batun sauya shekar da cewa suna yin makauniyar siyasa.

Kara karanta wannan

Tinubu zai mayar da babban birnin tarayyar Najeriya Legas? Sanata Shehu Sani

Sanusi II ya goyi bayan dauke wani sashe na CBN daga Abuja zuwa Legas
Sanusi II ya goyi bayan dauke wani sashe na CBN daga Abuja zuwa Legas, ya fadi dalili. Hoto: KC Nwakalor
Asali: Getty Images

Mayar da CBN Legas: Sanusi ya ce gwamnati ta yi dai dai

Yan Najeriya da dama sun soki yunkurin gwamnati na mayar da wani bangare na bankin CBN daga Abuja zuwa Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu ‘yan siyasar arewa sun yi tir da matakin, inda suka yi gargadin cewa zai haifar da illa a siyasance.

Sai dai Sanusi, wanda shi ne Sarkin Kano na 14, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce sauya shekar wani mataki ne mai ma'ana, The Nation ta ruwaito.

Ni ma na yi niyyar mayar da hedikwatar CBN zuwa Legas - Sanusi

A cewarsa:

"Matsar da wani bangare zuwa ofishin bankin na Legas (wanda ya fi babban ofishin Abuja girma) wani mataki ne mai ma'ana."

Ya ce shima ya yi niyyar daukar wannan matakin a sa'ilin da yake ofis amma bai samu isasshen lokacin ganin hakan ta tabbata ba.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun ki karbar cin hancin naira miliyan 1, sun kama dan bindiga a otal din Kaduna

Sanusi ya shawarci CBN da kada ta yi kasa a guiwa saboda matsin lamba na siyasa, yana mai cewa dole ne bankin ya kara kaimi wajen tabbatar da wannan matakin.

Yan sanda sun kama dan bindiga a wani otal din Kaduna

A wani labarin kuma, rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna ta ce ta kama wani dan bindiga da ke ayyukan garkuwa da mutane a dajin Kaduna, lokacin da ya ke shakatawa a wani otal.

Rundunar ta ce bayan kama shi ne ya yi kokarin ba shugaban ofishin 'yan sanda cin hancin naira miliyan daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel