Hadimin Ganduje kan lamuran Addini, Alibaba, ya handame N16m na addu'an Malamai kan cutar Korona

Hadimin Ganduje kan lamuran Addini, Alibaba, ya handame N16m na addu'an Malamai kan cutar Korona

Ana zargin Babban mai bada shawara ga gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, kan lamuran addini, Alibaba Agama-Lafiya, da laifin karkatar da miliyoyin kudin Malaman addini.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Alibaba ya handame kudin aka bashi ya rabawa Malamn da aka gayyata gidan gwamnatin jihar don gudanar da addu'a kan annobar cutar Korona.

Legit Hausa ta ruwaito ranar 30 ga Yuli cewa gwamnatin jihar Kano ta gayyaci akalla Malamai da Limamai 360 zuwa gidan gwamnati don gudanar da addu'a da saukar Al-Qur'ani na neman agajin Allah kan cutar Korona da matsalar tsaro a jihar.

Wakilin Daily Nigerian ya tattaro cewa Ganduje ya bada umurnin rabawa kowani Malami N50,000.

Kwamishanan lamuran addinin jihar, Muhammad Tahar Baba Impossible, ya tabbatar da cewa gwamnan ya bada umurnin a rabawa Malamai 360 da sukayi musharaka a taron addu'an dubu hamsin-hamsin.

Yayin nuna bacin ransa, Baba Impossible ya bayyana cewa sai da gwamna Ganduje yayi gargadin cewa kada a sake a rage kudin saboda na Malaman da sukayi taron adddu'an ne.

An tattaro cewa Alibaba Agama-Lafiya wanda ya jagoranci taron addu'an ya rabawa Malaman dubu biyar-biyar maimakon hamsin-hamsin.

Yayinda akayi lissafin N45,000 zuwa gida 360, an samu rage handame N16,200,000.

Daya daga cikin Limaman wanda yayi tattauna da Daily Nigerian kuma ya bukaci a boye sunansa yace gaskiya bai taba tunanin Alibaba zai taba aikata hakan ba.

Yace: "Nayi matuka mamaki da hakan. Dukkanmu mun san N50,000 akace a baiwa kowanne cikinmu, amma abin mamaki aka bamu N5,000."

"Ya baiwa yaronsa da wasu mutane biyu hakkin raba mana N5,000 kuma yayinda mukayi kokarin magana, sun rokemu cewa muyi shiri saboda mutum ne mai mutunci."

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Bayan shekara 1, an rantsar da zababbun yan majalisar dokokin Edo 12 mabiya Oshiomole (Hotuna)

Hadimin Ganduje kan lamuran Addini, Alibaba, ya handame N16m na addu'an Malamai kan cutar Korona
Hadimin Ganduje kan lamuran Addini, Alibaba, ya handame N16m na addu'an Malamai kan cutar Korona
Asali: Facebook

Duk yunkurin da aka yi na tuntubar Adama-Lafiya domin ta bakinsa ya ci tura yayinda aka samu layukan wayoyinsa a kashe.

Amma a ranar Laraba, Ali Baba Agama Lafia da kansa ya tabbatarwa manema labaran gidan rediyon Freedon cewa an baiwa Limaman dubu biyar-biyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng