Gwamna Abba Ya Fitar da Sanarwar Nadin Mukamai Yayin da SSG Ya Tafi Jinya a Saudi

Gwamna Abba Ya Fitar da Sanarwar Nadin Mukamai Yayin da SSG Ya Tafi Jinya a Saudi

  • Abba Kabir Yusuf ya sanar da cewa Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya karbi hutu domin ya yi jinya a kasar Saudi Arabiya
  • Abdullahi Musa wanda aka nada a matsayin shugaban ma’aikatan gwamnatin Jihar Kano zai kula da ofishin SSG
  • Sanusi Dawakin Tofa ya tashi daga Sakataren yada labarai sannan an nada shugabannin hukumomi da ma’aikatu

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Mai girma Abba Kabir Yusuf ya sanar da cewa Sakataren gwamnatin jihar Kano, Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya tafi asibiti a ketare.

A wani jawabi da ya fito daga ofishin Sanusi Bature Dawakin Tofa, an fahimci Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya je ganin likita a Saudi Arabiya.

Gwamnan Kano
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: @babarh
Asali: Twitter

Kamar yadda Sakataren yada labaran gwamnan Jihar Kano ya bayyana, Abdullahi Musa zai kula da ofishin Sakataren gwamnatin.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya tsokano Rigima da ikirarin babu aikin da Buhari ya yi a shekara 8

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: Abba ya ce HOS zai kula da aikin SSG, Bichi

Abdullahi Musa zai rike wannan matsayi na rikon kwarya ne zuwa lokacin da Dr. Baffa Bichi zai dawo daga asibiti, ya cigaba da aiki.

"Alhaji Abba Kabir Yusuf ya umarci shugaban ma’aikatan gwamnatin Jihar Kano, Abdullahi Musa, ya lura da ofishin Sakataren gwamnati.
An bada mukamin ne a sakamakon hutun jinya da Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya dauka, wanda ya bar kasar domin neman magani a Saudi Arabiya."

- Sanusi Bature Dawakin Tofa

Wasikar nadin Musa ta fito ne daga hannun Hon. Shehu Wada Sagagi a matsayinsa na shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano.

Shehu Wada Sagagi ya ce ana sa rai Musa zai rike kujerar na wasu ‘yan makonni.

Abba ya yi nadin mukamai a Kano

A wata sanarwar kuma, gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi wasu sababbin nade-naden mukami tare da yi wa wasu karin girma.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida ya kirkiri asibitin tafi da gidanka don amfanin Kanawa, ya tura sakon gargadi

Sanusi Dawakin Tofa ya samu karin matsayi daga Sakataren yada labarai zuwa Darekta Janar na harkar yada labarai da hulda da jama’a.

Wadanda Abba ya ba mukamai

1. Hon. Rabi'u Saleh Gwarzo – Kwamishina I a SUBEB

2. Injiniya Sarki Ahmad – Darekta Janar na aikin ‘Rural Access and Mobility’

3. Hon. Surajo Imam Dala – Darekta Janar na Talla da barace-barace a titi

4. Dr. Dahiru Saleh Muhammad – Shugaban hukumar makarantun kimiyya

5. Abubakar Adamu Rano – Mataimakin Darektan Rediyo Kano

6. Hajiya Hauwa Isah Ibrahim – Mataimakiyar Darektar ARTV

7. Dr. Gaddafi Sani Shehu – Mataimakin Darektan KHEDCO

Bayan haka an ji labari gwamna Abba ya nada masu ba shi shawara a kan harkokin Yarbawa, Ibo da sauran mutanen Arewa da ke zama a Kano.

Ga wadanda aka ba mukaman nan:

  1. Dr. Ibrahim Garba Muhammad
  2. Hon. Dankaka Hussain Bebeji
  3. Cif Chukwuma Innocent Ogbu
  4. Abdussalam Abdullateef
  5. Mr. Andrew Ma'aji
  6. Alh. Usman Bala
  7. Hajiya A'in Jafaru Fagge
  8. Hon. Isah Musa Kumurya
  9. Dr. Naziru Halliru
  10. Barr. Maimuna Umar Sharifai
  11. Hon. Danladi Karfi
  12. Gwani Muhammad Auwal Mukhtar
  13. Alhaji Ada'u Lawan

Kara karanta wannan

An yanka ta tashi: Tsohon Sanata ya kalubalanci nade naden mukaman Tinubu a NNPC

Kano 2023: Shari'ar Abba v APC a kotu

Ana da labarin yadda wasu korarrun jiga-jigan jam'iyyar NNPP su ke neman kawowa Abba Kabir Yusuf da Rabiu Kwankwaso matsala a siyasa.

Wadannan mutane da aka kora daga jam'iyya sun fara yaɗa cewa Abba ba cikakken 'dan NNPP bane kamar yadda kotu ta yi hukunci a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel