Gwamna Fintiri Ya Sha Alwashin Hukunta Binani da Wasu Kan Dalili 1 Tak, Ya Yi Alkawari

Gwamna Fintiri Ya Sha Alwashin Hukunta Binani da Wasu Kan Dalili 1 Tak, Ya Yi Alkawari

  • Bayan samun nasara a Kotun Koli, Gwamna Ahmadu Fintiri ya sha alwashin hukunta duk masu hannu a kokarin kwace masa kujera
  • Fintiri ya ce zai hukunta duk wadanda suka hada kai don ganin sun kawo cikas a kujerarsa a lokacin zabe
  • Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya ke jawabi bayan nasara a Kotun Koli a karon farko a Yola

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Adamawa – Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya sha alwashin hukunta ‘yar takarar APC, Aisha Binani.

Fintiri ya kuma ce zai hukunta kwamishinan zabe, Hudu Ari da sauran wadanda suka yi kokarin kwace masa kujerar a zabe.

Kara karanta wannan

Babban bankin Najeriya CBN ya gano wani dalili 1 tak da ke jawo faduwar darajar Naira

Gwamna Fintiri zai hukunta Binani da wasu kan zabe
Gwamna Fintiri ya yi magana a karon farko bayan nasara a Kotun Koli. Hoto: Ahmadu Fintiri.
Asali: Twitter

Mene Fintiri ya ce kan Binani da saura?

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya ke jawabi bayan nasara a Kotun Koli a karon farko.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

“Na kasance cikin natsuwa bayan kokarin kwacemin kujera ya ci tura duk wadanda suka yi kokarin hakan sun je kotu saboda rashin kunya.
“Dukkan wadanda suka hada kai da kwamishinan zabe, Hudu Ari da suka saka dimukradiyyar jihar cikin matsala za a hukunta su dai-dai yadda doka ta ce.
“Jihar Adamawa ta PDP ce kamar yadda zaben cike gurbi da Majalisar jiha ya nuna a ranar Asabar 3 ga watan Faburairu.”

Hudu Ari ya ayyana Binani wacce ta ci zabe

Fintiri ya kuma yi alkwarin ci gaba da mulkar jihar yadda ya dace musamman bangaren samar da ilimi kyauta, cewar Tribune.

Idan ba a manta ba, kwamishinan zaben, Hudu Ari ya ayyana ‘yar takarar jam’iyyar APC, Aisha Binani wacce ta lashe zaben gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Bincike: Yadda aka kashe naira biliyan 12 tare da cefanar da kadarorin Kotun Koli ba bisa ka'ida ba

Ari ya ayyana Binani ce duk da cewa a lokacin ana ci gaba da tattara sakamakon zaben jihar, cewar Daily Post.

Daga bisani, Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta rusa maganar Ari inda ta bayyana shi wanda bai halatta ba.

Jama’a sun tsare jami’an INEC

Kun ji cewa masu kada kuri’u sun tsare jami’an hukumar INEC yayin da ake ci gaba da zaben cike gurbi.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar 3 ga watan Faburairu a Jos ta Arewa inda suke zargin jami’an da kin kawo isassun kayayyakin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel