Bincike: Yadda Aka Kashe Naira Biliyan 12 Tare da Cefanar da Kadarorin Kotun Koli Ba Bisa Ka’ida Ba

Bincike: Yadda Aka Kashe Naira Biliyan 12 Tare da Cefanar da Kadarorin Kotun Koli Ba Bisa Ka’ida Ba

  • Ofishin Odita-Janar na Tarayya (OAuGF) ya bayyana cewa Kotun Kolin Najeriya ta kashe sama da naira biliyan 12 ba bisa ka’ida ba
  • Daga shekarar 2017 zuwa 2021, bincike ya nuna cewa akwai kadadorin da jami'an kotun suka karkatar da su don amfani kai da kai
  • Rahoton binciken ya kuma nemi a kwato wadannan kudade tare mayar da su asusun magatakardar kotun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Wani sabon bincike da ofishin babban mai bincike na kasa (OAuGF) ya yi, ya nuna yadda Kotun Koli ta kashe sama da naira biliyan 12 ba bisa ka'ida ba.

Rahoton binciken da aka fitar a watan Disamba 2023 ya kuma nemi a kwato wadannan kudade tare mayar da su asusun magatakardar kotun.

Kara karanta wannan

FAAN: Ministan Tinubu ya bayyana alfanun da za a samu kan mayar da ofishin Legas, ya fadi dalili

An tabfka babbar badakala a Kotun Koli daga 2017 zuwa 2021.
An tabfka babbar badakala a Kotun Koli daga 2017 zuwa 2021. Hoto: Supreme Court
Asali: Twitter

Rahoton dai ya yi bayani game da binciken da aka yi a ma'aikatu, hukumomi da sashe sashe na gwamnati kan kudaden shige da ficensu na 2020.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai binciken ya zurfafa a Kotun Koli inda aka bankado wasu kudade masu yawa da aka yi hada-hadarsu tsakanin 2017 zuwa 2021, Premium Times ta ruwaito.

Wadanda ke shugabantar kotun daga 2017 zuwa 2021

Babban magatakardar kotun, Hajo Sarki-Bello, ya karbi ragamar aiki a shekarar 2021, shekara daya bayan da aka tafka wannan barna karkashin Hadizatu Uwani-Mustapha.

Misis Uwani-Mustapha, wacce ta rike mukamin magatakardar kotun tsawon shekarun da aka yi badakalar ta yi ritaya a watan Yunin 2021.

Walter Onnoghen da Tanko Muhammad, tsaffin manyan jojin Najeriya daga 2016 zuwa 2022, su ne shugabannin Kotun Koli a lokacin da aka tafka barnar.

Mr Muhammad ya yi murabus a watan Yunin 2022 akan ikirarin rashin lafiya yana tsaka da fuskantar suka daga abokan aikinsa kan badakalar kudi.

Kara karanta wannan

Jerin kasashen duniya 5 da ya kamata ka ziyarta kafin su kara yawan jama'a

Hanyoyin da aka bi wajen karkatar da kudin

Abubuwan da rahoton ya nuna kan karkatar da naira biliyan 12.335 sun hada da biyan kudin kwangila alhalin babu bayanin hakan.

Karkatar da kadarorin gwamnati don amfanin kai da kai, tsugaga yawan kuɗin kwangila, ba da kwangila ba bisa ka'ida ba da sauransu.

Rahoton ya kuma bankado yadda aka sayar da kadarori hudu mallakar kotun a Legas.

Haka kuma, rahoton ya nuna cewa Kotun Koli ta kasafta tare da karbar naira miliyan 645 don siyan kayan aikin watsa labarai a shekarar 2017, amma ba ta siya ba.

Kotu ta daure matashin da ya ci bashin banki a Bauchi

A wani labarin, babbar kotu a jihar Bauchi ta ba da umurnin a garkame wani matashi mai suna Yusuf Aminu a gidan kaso bayan karbar bashi daga bankin FCMB.

An ruwaito cewa Aminu ya gaza biyan bashin bayan da ya cinye kudin ba tare da ya yi sana'ar da ya ce zai yi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel