Gwamna Ya Samu Ƙofar Runtumo Bashi a Jiharsa, Majalisa Ta Dakatar da Ɗan Majalisa Kan Abu 1

Gwamna Ya Samu Ƙofar Runtumo Bashi a Jiharsa, Majalisa Ta Dakatar da Ɗan Majalisa Kan Abu 1

  • Kakakin majalisar dokokin jihar Edo ya dakatar da ɗan majalisa ɗaya na tsawon wata uku bisa laifin yunkurin raba kan ƴan majalisa
  • Haka nan kuma majalisar ta amince da buƙatar Gwamna Obaseki na PDP na ciyo bashi domin gudanar da wasu ayyuka a jihar Edo da Abuja
  • Majalisar ta ɗauki waɗan nan matakan ne a zamanta na ranar Litinin, 29 ga watan Janairu, 2024 wanda Blessing Agbebaku ya jagoranta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Shugaban majalisar dokokin jihar Edo, Blessing Agbebaku, ya dakatar da mamba mai wakiltar mazaɓar Esan ta Kudu maso Gabas, Sunny Ojiezele, na tsawon watanni uku.

Agbebaku ya sanar da dakatar da ɗan majalisar ne bisa zarginsu da kokarin raɓa kawunan ƴa majalisa a zaman ranar Litinin, 29 ga watan Janairu, 2024, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya fusata, ya sanya dokar kulle a garuruwa biyu bayan faɗa ya kaure

Gwamna Godwin Obaseki.
Majalisa ta dakatar da mamba, ta amince gwamna ya karbo bashin makudan kuɗi Hoto: Godwin Obaseki
Asali: Facebook

Jim kaɗan bayan sanar da ɗaukar wannan mataki, shugaban majalisar ya umarci jami'an tsaro su tasa keyarsa zuwa wajen majalisar, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar dillancin labarai ta Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa Mista Ojiezele shine dan majalisa na farko da aka dakatar a majalisar dokokin jihar Edo ta takwas.

Gwamna Obaseki ya samu damar karɓo bashi

Majalisar ta amince da bukatar Gwamna Godwin Obaseki na runtumo rancen tallafin noma na Naira biliyan 2.2 tare da shirin biyan Naira miliyan 94.3 cikin watanni 24.

Har ila yau, majalisar ta amince da karɓo bashin Naira biliyan 9.1 na kwangila, kudi da lamunin banki daga bankin First Bank ga gwamnatin jihar Edo don gina wasu gidaje a Asokoro, Abuja.

Haka kuma ta amince da siyan motocin bas guda 50 na CNG na hukumar sufurin birnin Edo da gina tituna, da magudanan ruwa a sabon Coral City na Benin da dai sauransu

Kara karanta wannan

Majalisar dokokin jihar APC ta tabbatar da tsige shugaban majalisar, ta rantsar da sabo

Kotu kolo ta kori karar da aka kai Tinubu

A wani rahoton kuma Kotun Kolin Najeriya ta kori ƙarar da aka kalubanci nasarar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a zangon mulkin da ya fara na shekara huɗu.

Kotun ta kuma kori ƙarar da aka shigar da tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, Antoni Janar na ƙasa (AGF) da hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC).

Asali: Legit.ng

Online view pixel