Bayan Na Kano, Kotun Koli Ta Sake Sanya Ranar Raba Gardama a Shari'ar Neman Tsige Gwamnan Arewa

Bayan Na Kano, Kotun Koli Ta Sake Sanya Ranar Raba Gardama a Shari'ar Neman Tsige Gwamnan Arewa

  • Yayin da ake shirin yanke hukunci a jihar Kano, Kotun Koli ta sanya ranar raba gardama shari'ar zaben Plateau
  • Kotun ta sanya gobe Juma'a 12 ga watan Janairu a matsayin ranar yanke hukuncin zaben gwamnan PDP a jihar
  • Gwamna Caleb Mutfwang shi ke kalubalantar hukuncin Kotun Daukaka Kara da ta rusa zaben inda ta bai wa APC

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau - Kotun Koli ta sanya gobe Juma'a 12 ga watan Janairu ranar raba gardama a shari'ar zaben jihar Plateau.

Gwamna Caleb Mutfwang na jihar shi ke kalubalantar hukuncin Kotun Daukaka Kara da ta soke zabenshi, cewar Premium Times.

Kotun Koli ta shirya raba gardama a shari'ar zaben gwamnan Arewa
Kotun Koli ta sanya gobe Juma'a ranar raba gardama a shari'ar zaben gwamnan jihar Plateau. Hoto: Nentawe Goshwe, Caleb Mutfwang.
Asali: Twitter

Yaushe za a yanke hukunci a Plateau?

Kara karanta wannan

Kano: Kotun Koli ta tsayar da ranar yanke hukunci kan shari'ar Abba da Gawuna

Lauyan jami'yyar PDP a jihar, P. E Dakyen shi ya bayyana haka a yau Alhamis 11 ga watan Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

"Ku sani cewa za a yanke hukuncin shari'ar zaben jihar Plateau a gobe Juma'a 12 ga watan Janairu.
"Dukkan lauyoyinmu sun samu wannan sanarwa ta ranar yanke hukuncin."

Mene APC ke cewa kan hukuncin a Plateau?

Har ila yau, jami'yyar APC a bangarenta ita ma ta tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa a yau Alhamis 11 ga watan Janairu, cewar Punch.

Jam'iyyar ta roki magoya bayanta da su kwantar da hankulansu yayin da suke tsammanin hukuncin zai zo musu yadda suke so, cewar Leadership.

Sakataren yada labaran jami'yyar a jihar, Sylvanus Namang shi ya bayyana haka inda ya ce za su amince da duk hukuncin da aka yanke.

Kara karanta wannan

Bayan kama 8, Asirin masu hannu a kisan bayin Allah sama da 150 ya ƙara tonuwa a arewa

Ya ce:

"Yayin da Kotun Koli za ta yanke hukunci a shari'ar zaben jihar Plateau, muna kira ga magoya bayanmu su kasance masu bin doka.
"Duk hukuncin da kotun ta yanke, jami'yyar APC a matsayinta na mai bin doka za ta karbe shi hannu bibbiyu."

Gwamna Caleb ya tura sako ga Kotun Koli

A wani labarin, Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau ya roki Kotun Koli ta yi masa adalci a yayin yanke hukuncin shari'ar zaben jihar.

Gwamnan ya ce bai gamsu da hukuncin Kotun Daukaka Kara ba inda ta yi watsi da bakwai daga cikin hujjojinsa.

Wannan na zuwa ne yayin da ake dakon hukuncin Kotun Koli kan shari'ar zaben gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel