Zaben 2027: Jigon LP Ya Magantu Kan Yiwuwar Hadewar Atiku, Kwankwaso Da Peter Obi

Zaben 2027: Jigon LP Ya Magantu Kan Yiwuwar Hadewar Atiku, Kwankwaso Da Peter Obi

  • Farfesa Pat Utomi ya yi watsi da jita-jitar da ake ta yadawa kan cewa jam'iyyun adawa za su tsayar da mabambantan ƴan takarar shugaban ƙasa
  • Jigon na jam’iyyar LP ya bayyana cewa babban abin da jam’iyyun adawa suka fi mayar da hankali a kai shi ne samar da haɗin gwiwa mai ƙarfi don tunkarar jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027
  • Utomi ya zargi wasu kafafen yaɗa labarai da kitsa wata manufa ta raba kan jama’a ta hanyar rura wutar jita-jita game da ƴan takarar shugaban ƙasa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Farfesa Pat Utomi, shugaban ƙungiyar National Consultative Front (NCFront) ya bayyana cewa babban abin da manyan jam’iyyun adawa za su mayar da hankali a kai a 2027 shi ne kafa babbar jam’iyyar siyasa da za ta ƙwace mulki daga jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Kotun koli ta raba gardama a shari'ar zaben gwamnan APC a jihar Arewa

Ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da wasu ke ta raɗe-raɗin cewa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, Peter Obi na jam’iyyar LP, da kuma Rabi’u Kwankwaso na jam’iyyar NNPP sun fara shirin tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Utomi ya yi magana kan hadewar Atiku, Obi da Kwankwaso
Pat Utomi ya yi nuni da yiwuwar hadewar Atiku, Obi da Kwankwaso Hoto: Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso, Mr. Peter Obi
Asali: Facebook

Akwai yiwuwar hadakar Atiku, Obi da Kwankwaso - Pat Utomi

A cikin wata sanarwa a ranar Lahadi mai ɗauke da sa hannun Malam Hamisu San Turaki a madadin NCFront, Utomi ya yi nuni da cewa akwai ƙulla-ƙullar da kafafen yaɗa labarai ke yi, cewar rahoton Daily Independent.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa kafafen yaɗa labaran na yaɗa jita-jitar ne domin kawo cikas kan shirin haɗewa waje ɗaya da jam'iyyun adawan suke yi.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, shugabannin jam’iyyun adawa sun fi mayar da hankali wajen ƙarfafa ginshiƙinsu gabanin zaɓen 2027, ba wai tsayawa takarar muƙaman siyasa ba kamar yadda ake hasashe.

Kara karanta wannan

Ganduje ya bayyana gwamnoni, sanatoci da yan majalisar da za su dawo APC

NNPP Ta Buɗe Ƙofar Haɗaka da APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa Abdulmumin Jibrin dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji, ya ce kofar NNPP a bude take don yin haɗaka ko maja da jam'iyyar APC.

Jibrin, na hannun daman Rabiu Musa Kwankwaso kuma jigo a jam'iyyar NNPP, ya ce jam'iyyar ba za ta damu da hada hannu da PDP ko LP ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel