‘NNPP Ta Bude Kofar Hadaka da APC’, Dan Majalisar Kano Ya Shirya Addu’a Ta Musamman Ga Tinubu

‘NNPP Ta Bude Kofar Hadaka da APC’, Dan Majalisar Kano Ya Shirya Addu’a Ta Musamman Ga Tinubu

  • Wani mamba a majalisar wakilan tarayya, Abdulmumin Jibrin, ya gudanar da taron addu'o'i ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Jibrin wanda jigo ne a jam'iyyar NNPP, ya tara malamai don yin addu'a ga uban gidansa, Rabiu Kwankwaso, da kuma gwamnan Kano, Abba Kabir
  • A jawabinsa, Jibrin ya ce kofar jam'iyyar NNPP a bude take ga yin hadaka da jam'iyyar APC da ma duk wata jam'iyyar siyasa a Najeriya.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano, jihar Kano - Abdulmumin Jibrin dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji, ya ce kofar NNPP a bude take don yin hadaka ko maja da jam'iyyar APC.

Jibrin, na hannun daman Rabiu Musa Kwankwaso kuma jigo a jam'iyyar NNPP, ya ce jam'iyyar ba za ta damu da hada hanu da PDP ko LP ba.

Kara karanta wannan

Shari’ar Kano: ’Yan jam’iyyar NNPP sun yi ganganmin addu'o'i duk da gargadin 'yan sanda

Abdulmumin Jibrin/Majalisar tarayya/Jihar Kano/Rabiu Kwankwaso/Bola Tinubu
Dan majalisar ya tara sama da malamai 1,000 domin yin addu'a ga Kwankwaso, Tinubu da Abba Kabir. Hoto: @AbdulAbmJ
Asali: Facebook

Dan majalisar tarayya ya shirya taron addu'a ga Tinubu

Jibrin ya bayyana hakan yayin da ya hada kan sama da malamai 1,000 don gudanar da addu'o'i ga shugaban kasa Tinubu da Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron ya gudana ne a garinsa na Kofa, Bebeji, jihar Kano, a ranar Lahadi, 26 ga watan Nuwamba, Legit ta ruwaito.

A jawabinsa, Jibrin ya ce ba boyayyen abu bane alakarsa da Shugaba Tinubu ba. Ya kara da cewa Kwankwaso ne uban gidansa kuma zai ci gaba da martana alakarsa da mutanen biyu.

Tsohon mamba na jam'iyyar APC ya bayyana jam'iyyar NNPP a matsayin "jam'iyya ta amana" wacce za ta kasance mai sanya Najeriya gaba da komai.

Gwmnatin Ganduje ta dauki daliban JSS, dan shekaru 13 aikin gwamnati a Kano

A wanui labarin, gwamnatin Kano ta fallasa wata badakala da ta ce gwamnatin Abdullahi Ganduje ta yi na daukar ma'aikata, inda ta gano yara 'yan sakandire a masu daukar albashi.

Kara karanta wannan

Ganduje ya saka lalubule da tsohon shugaban kasa a gidansa da ke Abuja, bayanai sun fito

Akwai dubunnan mutane da gwamnatin Abba Kabir ke ganin gwamnatin baya ta dauka aiki ba bisa ka'ida ba, da wannan ta dakatar da albashin su, rahoton Legit Hausa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kafa wani kwamiti da zai tantance duk wasu ma'aikata da gwamnatin Ganduje ta dauka aiki a jihar don gano wadanda basu cancanta ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel