Cikakken Jerin Gwamnoni Jihohin 4 Da Za Su San Makomarsu a Kotun Ƙoli a Makon Nan

Cikakken Jerin Gwamnoni Jihohin 4 Da Za Su San Makomarsu a Kotun Ƙoli a Makon Nan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ana sa ran kotun kolin Najeriya za ta raba gardama kan sahihancin nasarar gwamnoni 21 a zaben da aka yi ranar 18 ga watan Maris, 2023.

A cewar rahoton The Nation, mafi yawan kararrakin da aka kalubalanci waɗan nan gwamnonin, kotun koli ta tsara sauraronsu a wannan makon da muka shiga.

Gwammonin da zasu san makomarsu a kotun koli.
Jerin Gwamnonin da Kotun Koli Zata Yanke Hukunci Kan Nasarar Su a Makon Nan Hoto: Celeb Mutfwang, Abba Kabir Yusuf, Dauda Lawal
Asali: Twitter

Gwamnonin da ke dab da sanin makomarsu sun haɗa da na Peoples Democratic Party (PDP), All Progressives Congress (APC), New Nigeria Peoples Party (NNPP) da Labour Party.

A tsare-tsaren kotun koli na mako, za a saurari kararrakin jihohin Ebonyi, Filato, Delta, Adamawa, Abia, Ogun, Kuros Riba da Akwa Ibom tsakanin yau Litinin 8 ga watan Janairu da Alhamis 11 ga watan Janairu, 2024.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar karshe ta neman tsige gwamnan PDP, ta ba da bahasi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa kotun kolin na iya yanke hukunci a kararrakin zaben gwamnan jihar Kano da Legas da sauransu a ranar Juma’a 12 ga watan Janairu.

Manyan shari'o'in zaben gwamnan da zasu fi ɗaukar hankali sun haɗa da;

1. Jihar Kano

Ranar 20 ga watan Satumba, 2023, kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamna ta tsige Abba Kabir Yusuf na NNPP daga kujerar gwamnan jihar Kano.

Idan zaku iya tunawa kotun ta ɗauki wannan matakin ne bayan soke halascin kuri'u 165,663 saboda babu hatimi da sa hannun hukumar zabe INEC.

Bayan haka kuma ta ayyana ɗan takarar APC, Dakta Nasir Yusuf Gawuna, a matsayin halastaccen zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano.

Gwamna Abba ya ɗaukaka kara zuwa kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja amma a nan ma ta kore shi daga mulki bisa hujjar cewa shi ba mamban NNPP bane a lokacin da ya nemi takara.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta tanadi hukuncin karshe kan nasarar Gwamnan PDP a jihar arewa

Bai haƙura ba, Gwamnan ya sake ɗaukaka ƙara zuwa kotun koli kuma nan ba da jimawa ba zai san makomarsa.

2. Jihar Filato

Gwamna Celeb Mutfwang na PDP na ɗaya daga cikin waɗanda ake sa ran zasu san makomarsu a kotun koli cikin makon nan

Mutfwang, wanda da fari ya samu nasara a kotun zaɓe, kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta tsige shi saboda jam'iyyar PDP ba ta da halastaccen tsarin shiga zaɓe.

Bisa rashin gamsuwa da hukuncin, Gwamna Mutfwang ya garzaya kotun koli ya shigar da ƙarar da ta kalubanci hukuncin karamar kotu.

3. Jihar Nasarawa

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ne ya lashe zaɓen 18 ga watan Maris amma ɗan takarar PDP, David Ombugadu, ya ƙalubalance shi a kotu.

A watan Oktoba, 2023, kotun zaɓe ta tsige Gwamna Sule kana ta ayyana Ombuhadu a matsayin wanda ya ci zaɓe saboda an yi maguɗin kuri'u.

Kara karanta wannan

Gwamna Bello ya tsige sarakuna 3 daga karagar mulki, ya yi muhimmin garambawul

Sai dai gwamnan ya samu sa'a a kotun daukaka kara yayin da kotun ta soƙe korarsa a ranar Alhamis 23 ga watan Nuwamba.

Jam’iyyun PDP da Ombugadu sun garzaya kotun koli domin neman haƙƙinsu, kuma hukuncin na ɗaya daga cikin wanda mutane da yawa ke jira su ji.

4. Jihar Zamfara

Dauda Lawal na jam’iyyar PDP ya kayar da gwamnan APC mai ci, Bello Matawalle, a zaben gwamnan jihar Zamfara da aka yi ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Sai dai Matawalle, wanda yanzu haka minista ne a karkashin Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya tunkari kotun zaɓe domin kalubalantar nasarar Lawal.

Kotun ta yanke hukuncin tabbatar da nasarar Lawal, amma Matawalle da jam’iyyar APC sun garzaya kotun daukaka kara, inda aka tsige Lawal.

Ta umarci hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta INEC ta canza sabon zabe a karamar hukumar Maradun da wasu yankuna a Bukkuyum da Birnin Magaji.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Jerin Muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Ministar da Tinubu ta dakatar

Amma Gwamna Lawal da PDP suka ɗaukaka kara zuwa kotun koli, inda suke fatan kotun mai daraja ta ɗaya ta dawo musu da nasara.

Muhimman abubuwa game da Edu

A wasu rahoton kuma ranar Litinin, 8 ga watan Janairu, 2024, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar da Betta Edu, ministar harkokin jin ƙai da yaye talauci.

Legit Hausa ta tattaro maku wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da dakatacciyar ministar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel