Kotun Koli Ta Tanadi Hukunci Kan Shari'ar Karshe Ta Neman Tsige Gwamnan PDP, Ta Ba da Bahasi

Kotun Koli Ta Tanadi Hukunci Kan Shari'ar Karshe Ta Neman Tsige Gwamnan PDP, Ta Ba da Bahasi

  • A yau Talata ce 9 ga watan Janairu Kotun Koli da ke zamanta a Abuja ta duba shari'ar zaben gwamnan jihar Delta
  • Kotun ta tanadi hukunci kan shari'ar da ake yi tsakanin PDP mai mulki da kuma APC da LP da kuma SDP
  • A kwanakin baya, Kotun Daukaka Kara da ke Legas ta tabbatar da nasarar Gwamna Sheriff Oborevwori a matsayin gwamnan jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Delta, Punch ta tattaro.

Kotun ta tanadi hukuncin ne yayin da dan takarar jam'iyyar APC a zaben, Ovie Omo-Agege ya shigar da korafi kan zaben.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta tanadi hukuncin karshe kan nasarar Gwamnan PDP a jihar arewa

Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan PDP
Kotun Koli ta shirya raba gardama a zaben gwamnan jihar Delta. Hoto: Sherrif Oborevwori, Ovie Omo-Agege.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke a baya?

Har ila yau, dan takarar jam'iyyar LP, Ken Pele da na jam'iyyar SDP, Kenneth Gbaji sun kalubalanci zaben da aka gudanar a watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kwanakin baya, Kotun Daukaka Kara da ke Legas ta tabbatar da nasarar Gwamna Sheriff Oborevwori a matsayin gwamnan jihar.

Har ila yau, kotun ta yi fatali da korafe-korafen 'yan takarar sauran jam'iyyun guda uku saboda rashin gamsassun hujjoji, cewar Channels TV.

Yawan kuri'un da ko wane dan takara ya samu a zabe

Oborevwori na PDP ya samu kuri'u 360,234 yayin da mai bi masa, Ovie Omo-Agege na APC ya samu kuri'u 240,229 a zaben.

Yayin da Ken Pela na LP ya samu kuri'u 48,027 sai kuma dan takarar jam'iyyar APGA, Great Ogboru ya samu kuri'u 11,021 a zaben, The Nation ta tattaro.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin gwamnonin jihohi 4 da za su san makomarsu a Kotun Koli a makon nan

Kotun Koli ta tanadi hukunci kan zaben Ebonyi

A wani labarin, Kotun Koli a jiya Litinin 8 ga watan Janairu ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Ebonyi.

A baya Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Francis Nwifuru na jami'yyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna.

Har ila yau, kotun ta yi watsi da korafin dan takarar jam'iyyar PDP, Chukwuma Odili da kuma jami'yyarsa saboda rashin gamsassun hujjoji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel