Gwamnan Bello Ya Tsige Sarakuna 3 Daga Karagar Mulki, Ya Yi Muhimmin Garambawul

Gwamnan Bello Ya Tsige Sarakuna 3 Daga Karagar Mulki, Ya Yi Muhimmin Garambawul

  • Gwamna Yahaya Bello ya tsige sarakuna uku sannan kuma ya naɗa sabon sarkin ƙasar Ebira a jihar Kogi
  • A cewarsa, gwamnati ta ɗauki wannan matakin ne bayan nazari da bin matakai da ƙa'idodjin kundin dokokin sarakunan jihar
  • Wannan na zuwa ne watanni ƙalilan bayan zaben gwamnan jihar Kogi wanda aka yi a watan Nuwamba, 2023

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya nada Alhaji Ahmed Tijani Anaje, tsohon Ohi na Okenwe, a matsayin sabon Sarkin ƙasar Ebira watau Ohinoyi na Ebiraland.

Dakta Ado Ibrahim, tsohon Ohinoyi na Ebiraland ya rasu ne a ranar 29 ga Oktoba, 2023, bayan doguwar jinya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yana dab da sauka mulki, Gwamna Bello ya naɗa sabbin shugabannin ƙananan hukumomi kan abu 1

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi.
Gwamna Yahaya Bello Ya Tsige Manyan Sarakuna 3, Ya Nada Sarkin Ebiraland Hoto: Yahaya Bello
Asali: Facebook

Bayan rasuwarsa, akalla mutane 70 ne suka nuna sha’awarsu ta maye gurbinsa, a cewar Alhaji Yunusa Sule, Sakataren Masarautar Ebiraland.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma a ranar Litinin, 8 ga watan Janairu, 2024 Gwamna Bello ya sanar da naɗin Alhaji Anje a matsayin wanda zai maye gurbin karagar mulkin Ebiraland.

Bello ya sauke Sarakuna 3

Gwamnan ya kuma tsige babban sarki kuma Ohimeghe Igu na Koton-Karfe, Alhaji Abdulrazak Isa Koto, tare da wasu sarakunan gargajiya guda biyu a jihar.

An sanar da korar Ohimeghe Igu na Koton-Karfe, wanda kuma shi ne shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta Lokoja/Kogi a taron majalisar zartarwa ta jiha (SEC) ranar Litinin.

A rahoton Leadership, Gwamna Yahaya Bello ya ce:

“An cire Mai Martaba Alhaji Abdulrazaq Isah Koto, Ohimege-Igu Koton-Karfe, wanda kuma shi ne shugaban majalisar gargajiya ta ƙaramar hukumar Lokoja/Kogi, kuma za a maida shi ƙaramar hukumar Rijau a jihar Neja.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin gwamnonin jihohi 4 da za su san makomarsu a Kotun Koli a makon nan

"Haka nan mun tsige mai martaba Sam Bola Ojoa, Olu Magongo na Magongo, kuma za a kai shi garin Salka, karamar hukumar Magama ta jihar Neja.
"Bugu da ƙari an tsige mai martaba Samuel Adayi Onimisi, Obobanyi na Emani, kuma za a tasa ƙeyarsa zuwa Doko, karamar hukumar Lavun ta jihar Neja.”

Bello ya ƙara da bayanin cewa gwamnatinsa ta cimma wannan matsaya ne bayan bin dukkan matakan doka da ƙa'idojin naɗin sarakuna a jihar Kogi.

Kotu ta yanke hukunci kan ƙarar Emefiele

A wani rahoton na daban babbar kotun Abuja ta yanke hukunci kan ƙarar tauye haƙƙin ƴancin walwala da tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya shigar.

Alkalin kotun ya bayyana garƙame Emefiele na tsawon wata 5 da hukumomi suka yi a matsayin wanda ya saɓa wa doka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel