Ministan Shugaba Tinubu Ya Canza Jam'iyya a Hukumance, Ya Bayyana Dalili 1 Tal

Ministan Shugaba Tinubu Ya Canza Jam'iyya a Hukumance, Ya Bayyana Dalili 1 Tal

  • Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce ya sake komawa jam'iyyar APC ne domin ya taimakawa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu
  • Adelabu ya bayyana cewa komawarsa jam'iyyar APC ba ta da alaƙa da burin zama magajin Gwamna Seyi Makinde a zaɓen 2027
  • Ya ƙara da cewa ya ɗauki wannan matakin ne domin miƙa hannun abota da kuma sasantawa da dukkan mambobin APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Oyo - Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana asalin dalilin da ya sa ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga jam’iyyar Accord Party.

Adelabu ya ce ko kaɗan bai koma APC da nufin ya zama magajin gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo a babban zaɓen 2027 ba, inji rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Ana zargin Shugaba Tinubu da rura wutar rikici a jihar PDP, bayani sun fito

Ministan Tinubu ya koma APC a hukumance.
Ministan Bola Tinubu, Adelabu Ya Bayyana Dalilin da Ya Sa Ya Koma APC Hoto: Bayo Adelabu
Asali: Facebook

Ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga ɗumbin magoya bayan jam'iyyar a wurin bikin sauya shekarsa a hukumance a sakatariyar APC da ke Oke-Ado, Ibadan, ranar Juma’a, 15 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene asalin dalilin da ya sa ministan ya koma APC?

A jawabinsa a wurin taron, ministan ya bayyana cewa ya ɗauki matakin komawa APC ne domin ya taimakawa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu.

A cewar Adelabu, tun farko bai fice daga APC saboda dalilin cewa yana da matsala da jam'iyyar ko wasu mambobinta na jihar Oyo ba.

A kalamansa, Minista Adelabu ya ce:

"Na dawo ba wai domin ina da burin tsayawa takarar gwamna a 2027 ko kwace iko da jam'iyya ba, sai don cewa ina da yaƙinin wannan ce jam'iyyar da ta ɗora shugaban ƙasa, Bola Tinubu a kan mulki."

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC ta daina boye-boye, tayi wa Ministan Tinubu tayin da zai jawo ya bar PDP

"Kuma ya kamata mu taimaka masa ya cika alkawurran da ya ɗauka. Yanzu ba lokacin siyasa bane, lokaci ne na shugabanci kuma Tinubu na buƙatar goyon bayanmu."
"Na dawo APC ba wai don na kwace iko da ita a Oyo ko na rushe shugabannin jam'iyya ba, mun dawo ne mu ƙara kulla dangantaka da kuma sasantawa."

Gwamna Fubara ya yi sabon jawabi

A wani rahoton na daban Rigima tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas da magabacinsa, Nyesom Wike, ta ƙara ƙamari a jihar mai arzikin man fetur.

Gwamna Fubara ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta kare muradan al'ummar jihar Ribas ta kowane hali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel