Kotun Daukaka Kara Ta Kori Kakakin Majalisar Bauchi

Kotun Daukaka Kara Ta Kori Kakakin Majalisar Bauchi

  • Kotun Daukaka Kara mai zamanta a Abuja ta yanke hukunci kan zaben mazabar Ningi ta Tsakiya da ke karamar hukumar Ningi, jihar Bauchi
  • Kotun ta kori dan majalisar mazabar, Suleiman Abubakar, wanda kuma shi ne kakakin majalisar dokoki ta jihar Bauchi
  • Wannan hukuncin a cewar kwamitin mutum uku, an yanke shi ne saboda samun kura-kurai da aka tafka yayin gudanar da zabe a mazabar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Bauchi - Rahotannin da muke samu yanzu na yin nuni da cewa Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta kori kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Abubakar Suleiman.

Wani kwamitin mutum uku a ranar Juma'a ya yanke hukuncin cewa zaben da Suleiman ya ci a mazabar Ningi ta Tsakiya na cike da kura-kurai.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin da suka yi nasara a Kotun Daukaka Kara kawo yanzu

Abubakar Suleiman/Kotun Daukaka Kara
Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta kori kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Abubakar Suleiman. Hoto: Ibrahim Miji
Asali: Facebook

Dalilin da ya sa kotu ta kori Suleiman

Kotun Daukaka Kara ta bayar da umarnin sake zabe a rumfunan zabe 10 da ke mazabar kakakin majalisar, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani bangaren, shugaban kwamitin shari'a kan lamarin ya gargadi hukumar zabe mai zaman kanta ta (INEC) da ta gudanar da al’amuranta kamar yadda doka ta tanada domin kaucewa jefa kasar nan cikin mawuyacin hali.

Da yake yanke hukunci a karar da aka shigar kan zaben mazabar Ningi ta Tsakiya, ya ce yadda INEC ta gudanar da zabukan 2023 ba yabo ba fallasa, The Nation ta ruwaito.

Kotu tabbatar da nasarar Gwamna Mohammed na Bauchi

A ranar Juma'a 18 ga watan Maris, 2023 Legit Hausa ta kawo labarin yadda Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta tabbatar da nasarar Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi a zaben gwamnan jihar, Legit Hausa ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu: Ministan Tinubu na shirin murabus yayin da ya karbi shaidar zama Sanata, Hotuna sun fito

Dan takarar gwamna a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Sadique Abubakar, ya daukaka karar biyo bayan hukuncin kotun kararrakin zabe da ta tabbatar da nasarar Mohammed.

Mai shari’ar kotun ya karanta hukuncin ne a kan korafin da mai daukaka karar ya shigar gaban kotun.

Sadique ya gaza gabatar da kwararan hujjoji

A kara ta daya, mai shigar da karar ya roki a soke zaben saboda ba a cike fom da takardun da aka yi amfani da su a zaben yadda ya kamata ba, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Kotun ta yanke hukuncin cewa wanda ya shigar da karar ya gaza gabatar da hujjoji kan wannan zargi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel