Abiola Ajimobi: Ganduje da iyalinsa sun je ta'aziyya wurin sirikansu
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya kai ziyarar ta'aziyya gidan iyalan sirikinsa, Sanata Abiola Ajimobi, wanda ajali ya katsewa hanzari a ranar Alhamis bayan fama da cutar korona.
Wannan rahoto na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban dandalan sada zumunta na jihar Kano, Basiru Yusuf Shuwaki ya fitar kan shafinsa na Twitter.
A sakon da Shuwaki ya wallafa, ya bayyana cewa Gwamna Ganduje da tawagarsa, sun je ta'aziyyar ne a ranar Asabar, 27 ga watan Mayu.
Cikin tawagar da suka je ta'aziyyar tare da Gwamna Ganduje sun hadar da mai dakinsa, Farfesa Hafsatu Ganduje da kuma sauran 'ya'yansu.
Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, Gwamnan da tawagarsa sun je gidan iyalan marigayi Sanata Ajimobi da ke jihar Legas domin mika gaisuwarsu, inda a nan ne mai yankan kauna ta katse masa hanzari.
Idris Ajimobi, wanda ya kasance mijin 'yarsu, Fatima Ganduje, shi ne ya tarbi tawagar gwamnan.
Haka zalika, a ranar Juma'a 26 ga watan Yuni, tawagar wasu gwamnonin jam'iyyar APC, suka kai ziyara har fadar gwamnatin Kano domin yi wa Ganduje ta'aziyya ta mutuwar sirikinsa.
Gwamnonin biyar wanda Mai Mala Buni na jihar Yobe ya jagoranci tawagarsu sun hadar da gwamnan jihar Ekiti, Fayemi Kayode da gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu.
Sauran 'yan tawagar sun hadar da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da kuma takwaransa na jihar Neja, Abubakar Sani Bello.
KARANTA KUMA: Ana sa'insa tsakanin gwamnatin Oyo da iyalan Ajimobi kan wurin da za a binne gawarsa
Legit.ng ta ruwaito cewa, binne gawar tsohon gwamnan jihar Oyo, a ranar Lahadi a garin Ibadan babban birnin jihar.
An yi wa Ajimobi jana'iza a bisa tanadi da koyarwar addinin musulunci. Sannan an binne shi a gidansa da ke 6th Avenue, Layin Yemoja na Unguwar Oluyole da ke Ibadan cikin yanayi na tsaro kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Gwamnatin jihar ta Oyo ta ki amincewa a binne marigayin a gidansa da ke Unguwar Agodi GRA saboda ana shariar a kotu game da gidan duk da cewa nan iyalansa suka fi so.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng