“Ko Na Yi Zabe Ko Ban Yi Ba Bai Da Amfani”: Dino Melaye Ya Magantu Kan Yadda APC Ta Murde Zaben Kogi

“Ko Na Yi Zabe Ko Ban Yi Ba Bai Da Amfani”: Dino Melaye Ya Magantu Kan Yadda APC Ta Murde Zaben Kogi

  • Dan takarar PDP, Dino Melaye ya ce kuri'arsa ba za ta kawo wani banbanci ba a zaben gwamnan jihar Kogi da aka yi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, 2023
  • Melaye yi wannan furuci ne a wata hira da aka yi da shi, kasa da awanni 24 bayan INEC ta ayyana dan takarar APC, Usman Ododo, a matsayin wanda ya lashe zaben Kogi
  • Tsohon sanatan ya jaddada cewar kuri'arsa bata da amfani a tsarin zaben da aka kammala kwanan nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Kogi, Lokoja - Daga karshe, dan takarar PDP, Sanata Dino Melaye ya magantu game da kuri'arsa a aben gwamnan jihar Kogi da aka gudanar a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

Dino Melaye ya ce kuri'arsa bata da amfani a zaben gwamnan Kogi da aka kammala
“Ko Na Yi Zabe Ko Ban Yi Ba Bai Da Amfani”: Dino Melaye Ya Magantu Kan Yadda APC Ta Murde Zaben Kogi Hoto: Dino Melaye
Asali: Facebook

Dino ya jaddada cewar APC ta murde zaben Kogi, ya yi karin bayani

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: INEC Ta Ayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Bayelsa

Tsohon sanatan na Kogi ya amsa wata gayyatar hira da Channels TV a ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamba, yana mai cewa kada kuri'arsa ko akasin haka a zaben da aka kammala bai da amfani.

Dan takarar gwamnan na PDP ya kuma yi bayanin cewa an yi masa magudi a zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ku tuna cewa PDP ce ta zo ta uku a zaben da kuri'u 46,362 yayin da dan takarar APC Usman Ododo ya lashe abe a jihar ta yankin Arewa ta Tsakiya.

Duk da ikirarin cewa Melaye bai kada kuri'arsa ba a yayin zaben na ranar Asabar, dan takarar na PDP ya yi korafin cewa bai da amfani a shirin abubuwa.

Tsohon dan majalisar ya ce:

"Batun yin zabe ko rashin yin zabe baida wani matsayi na doka. Mutane sun lashe zabe a gidan gyara hali.

Kara karanta wannan

Dama Dino Melaye bai cancanci zama gwamna ba, Wike ya tono asirin dan takarar gwamnan PDP a Kogi

“A bisa doka, ba shi da wani tasiri ga zaben. Ko na kada kuri’a ko ban kada kuri’a ba, bai da amfani."

Ya kuma yi zargin cewa wasu magauta a siyasa sun hadu sannan suka yanke shawarar cewa "sai ya zama na uku" a takarar zaben na ranar Asabar.

Dino ya ba INEC wa'adin kwana 7

A wani labarin, mun ji cewa dan takarar Gwamna a inuwar jam'iyyar PDP a zaɓen jihar Kogi, Sanata Dino Melaye, ya bai wa hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) wa'adi ta duba kokensa.

Sanata Melaye ya bayyana cewa wa'adin kwana Bakwai kacal ya ɗibarwa INEC ta sake nazari da duba kan zaɓen Gwamnan da aka kammala a jihar Kogi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng