Zaben Kogi: a Karshe, Dino Ya Yi Martani Kan Dokuwa da Yake a Zabe, Ya Fadi Abin da INEC Za Ta Yi

Zaben Kogi: a Karshe, Dino Ya Yi Martani Kan Dokuwa da Yake a Zabe, Ya Fadi Abin da INEC Za Ta Yi

  • Dino Melaye, dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Kogi ya yi korafi kan zaben da ake yi a jihar
  • Dino ya bukaci hukumar zabe ta soke zabukan da aka gudanar saboda samun sakamako tun kafin a fara zabe
  • Wannan na zuwa ne bayan dan takarar jam'iyyar APC a jihar, Usman Ododo na ci gaba da basu kaya a zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi - Dan takarar jam'iyar PDP a zaben gwamnan jihar Kogi, Dino Melaye ya yi martani kan yadda zaben ke tafiya.

Melaye ya kiraye hukumar zabe ta INEC da ta soke wannan zabe na murdiya da ake yi, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Zaben Kogi: INEC ta fitar da sabuwar sanarwa kan sake zabe a jihar Kogi, ta fadi ranar da za a yi

Dino ya ce sakamakon zaben ya bayyana tun kafin a fara kada kuri'u a jiya Asabar 11 ga watan Nuwamba a jihar.

Dan takarar ya bayyana haka ne a taron manema labarai a yau Lahadi 12 ga watan Nuwamba a birnin Lokoja da ke jihar.

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Jiya ba a yi zabe a kananan hukumomi 5 ba dake mazabar jihar Kogi ta Tsakiya.
"Abin mamaki a karshe, an tantance masu zabe ba tare da na'urar tantancewa ta BVAS ba a zaben."
"Ya kamata INEC ta soke zabukan saboda sakamakon zabe ya bayyana da yawan kuri'u tun kafin fara zabe."

Melaye ya kara da cewa wurare da dama da yaci zabe an fada wa wakilansa cewa babu isassun takardu da za a cike sakamakon, cewar Arise TV.

Ya ce an kama jami'an INEC da masu bautar kasa da shiryayyen sakamakon zabe kafin fara zabe da kuma naira miliyan daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.