INEC Ta Ayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Bayelsa

INEC Ta Ayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Bayelsa

  • A karshe an ayyana Douye Diri na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Bayelsa da aka yi a ranar Asabar
  • Baturen zaben jihar, Obo Effanga, ya ayyana Diri a matsayin wanda ya lashe zaben bayan ya lashe zabe a kananan hukumomi shida a jihar
  • Diri, wanda shine gwamna mai ci a jihar yanzu, ya lashe zabensa karo na biyu, ya kada Timipre Sylva na APC da Obo Effanga na jam'iyyar Labour

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya (INEC) ta ayyana Duoye Diri na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Bayelsa.

Diri, wanda ya yi takara don neman zarcewa karo na biyu a ofis, ya samu kuri'u 175,196 inda ya kada babban abokin hamyarsa, Timipre Sylva na jam'iyyar APC wanda ya samu kuri'u 110,108 kamar yadda Legit Hausa ta tattaro daga Channels Television.

Kara karanta wannan

Zaben Bayelsa: Bayan tattara sakamakon kananan hukumomi, an fadi wanda ke kan gaba da kuri'u dubu 65

Diri ya lashe zaben gwamnan jihar Bayelsa
Gwamna Duoye Diri na APC ya lashe zaben gwamnan jihar Bayelsa. Hoto: Douye Diri
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanene Diri, dan PDP da aka sake zaba gwamnan Bayelsa?

Gwamna Diri, wanda ya zama gwamna biyo bayan hukuncin Kotun Koli a 2019, ya yi nasara kan Sylva, tsohon gwamnan jihar kuma tsohon karamin ministan albarkatun man fetur.

Kotun Kolin ta soke zaben wanda ya lashe zaben 2019, David Lyon bayan an gano mataimakinsa ya gabatarwa INEC takardan karatu na bogi.

Gwamnan na PDP yana majalisa a matsayin sanata kafin babban kotun na kasa ta yanke hukuncin da ya soke takarar Lyon da mataimakinsa kwanaki kadan kafin rantsar da su.

Wanene Sylva, dan takarar gwamnan Bayelsa karkashin APC?

A bangarensa, Babban kotun tarayya a Abuja ta soke takarar Sylva saboda an taba rantsar da shi a matsayin gwamna har sau biyu kuma rantsar da shi sau uku zai zama saba doka.

Kara karanta wannan

Zabe ya kammala a Kogi, INEC ta sanar da wanda ya lashe zabe, ya fi kowa adadin kuri'u

Sai dai, Kotun Daukaka Kara ta Abuja ta soke hukuncin karamar kotun. Ta jadada Sylva a matsayin dan takarar gwamna na APC a zaben jihar Bayelsa na 2023.

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel