Zabukan Gwamnoni na Kogi, Imo da Bayelsa Kai Tsaye
Barka da zuwa shafin rahotanni kai tsaye na zabukan gwamnonin jihohin Kogi, Bayelsa da Imo na shekarar 2023!
Ku kasance tare da mu don samun bayanai kai-tsaye a dukkan jihohin uku a Najeriya inda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC), ke gudanar da zabukan da ba a yinsu tare da na kasa.
Ka rika sabunta na'urar shiga yanar gizonka don samun sabbin
Dino Melaye ya lashe mazaɓarsa a Kogi
Ɗan takarar Gwamna a inuwar jam'iyyar PDP a zaben jihar Kogi, Sanata Dino Malaye, ya lashe zaɓe a rumfar da ya kaɗa kuri'arsa a ƙaramar hukumar Ijimu.
PU: Open space, Iluafon quarters, RA: Aiyetoro 1, Ijumu LGA, Kogi
APC - 22
PDP - 210
SDP - 1
PRP - 2
NRM - 1
ADP - 1
ADC - 7
Har yanzu ba a fara zaɓe a wasu rumfunan zaɓe a Bayelsa ba
Har yanzu ba a fara gudanar da zaɓe a wasu rumfunan zaɓe a da ke ƙaramar hukumar Southern Ijaw a jihar Bayelsa.
A rumfunan zaɓe na 007, 0028 da ke gunduma ta 014 ba bu jami'an hukumar INEC ko kayayyakin zaɓe a wajen.
Jam'iyyu na siyan kuri'a kan N16,000
A rumfar zaɓe ta 16, gunduma ta 13, ƙaramar hukumar Ogbia a jihar Bayelsa an ga wakilin jam'iyyar yana miƙa wa mai kaɗa kuri'a kuɗi.
Rahotanni sun bayyana cewa jam'iyyun siyasa siyan kowace ƙuri'a ɗaya kan kuɗi N16,000, kamar yadda The Cable ta tattaro.
Dino Melaye ya kauracewa zaben jihar Kogi
Dan takarar jam’iyyar PDP, Dino Melaye ya kauracewa zaben da ake gudanarwa a jihar Kogi.
Melaye na zargin an riga an kamala zaben tun kafin a fara kada kuri’u shi yasa ya kauracewa zaben.
The Nation ta tattaro cewa Melaye ba ya mazabar shi da ke karamar hukumar Ijumu a jihar.
Zabukan Imo, Bayelsa da Kogi: APC ta bude ofishin sa ido kan yadda zabe ke gudana
Jam’iyyar APC ta bude ofishin sa ido kan yadda zabe ke gudana a jihohin Bayelsa, Imo da Kogi.
Jam’iyyar mai mulki ta tabbatar da hakan a cikin wata wallafa da ta yi a shafinta na X a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.
An tattaro cewa an bude ofishin ne a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja.
Dan takarar PDP a zaben Imo, Anyanwu ya kada kuri'a
Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben jihar Imo, Sanata Samuel Anyanwu ya kada kuri'arsa.
Anyanwu ya kada kuri'ar ce a mazabarshi ta 012 da ke makarantar Amimo a karamar hukumar Ikeduru a jihar Imo.
Dole a dakatar da zaɓukan Imo, Kogi da Bayelsa da sauransu - Jonathan
Tsohon shugaban ƙasa, Dakta Goodluck Ebele Jonathan, ya buƙaci majalisar tarayya ta fara aikin dakatar da gudanar zaɓukan da ake yi ba tare da babban zaɓen ƙasa ba.
Jonathan ya yi wannan furucin ne jim kaɗan bayan kaɗa kuri'arsa a zaben Gwamnan jihar Bayelsa da ke gudana yau Asabar, 11 ga watan Nuwamba.
Ya ce ya damu matuka da waɗannan zaɓuka da ake yi a lokaci daban domin sun saba wa tsarin duniya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Tsohon shugaban ya kuma taya ɗaukacin mazauna jihohin Imo, Kogi da Bayelsa yayin da suka fita zaɓen sabbin shugabannin da zasu jagorance su tsawon shekaru 4.
Ajaka na jam'iyyar SDP ya kada kuri'a a Kogi
Dan takarar jam'iyyar SDP, Murtala Ajaka ya kada kuri'arsa a mazabar shi a jihar Kogi.
Ajaka ya kasance daya daga cikin manyan 'yan takara da ake fafatawa da su a wannan zabe.
Rikici ya ɓarke a wata rumfar zaɓe a Bayelsa
Wani rahoto da ke fitowa ya tabbatar da barkewar rikici a yankin Agudama-Ekpetiama na jihar Bayelsa.
An tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, lokacin da jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ke kafa tantin su domin fara zaɓe.
Sai dai a lokacin da faɗa ya barke tsakanin matasan yankin, jami’an INEC sun yi sauri sun koma cikin kwale-kwalen su.
Gwamna Diri na Bayelsa ya kada kuri'a a mazabarshi
Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya kada kuri'a a zaben gwamnan a jihar, cewar TheCable.
Diri ya kada kuri'ar ce a mazabar Sampou/Kalam rumfa ta 4 a karamar hukumar Kokoluma/Opokuma.Diri ya kada kuri'ar ce a mazabar Sampou/Kalam rumfa ta 4 a karamar hukumar Kokoluma/Opokuma.
Zaɓen Kogi: Jami’an INEC sun maƙale, sun rasa motocin zuwa rumfunan zabe
Jami’an hukumar zaɓe mai zaman kanta da aka tura rumfunan zaɓe daban-daban a fadin Lokoja suna maƙale a makarantar tunawa da Ajayi Crowther.
Jami’an sun kasance a wurin domin karɓar kayayyakin zaɓen da za a gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba a jihar.
Daga cikinsu akwai ƴan bautar ƙasa da ma’aikatan wucin gadi da hukumar ta ɗauko domin gudanar da zaɓen.
Duk da cewa jami'an sun karɓi kayayyakin zaben, har yanzu suna nan a makale saboda babu wata motar da za ta yi jigilarsu zuwa rumfunan zaɓe.
An ji wani jami’i yana sanar da wasu jami’an cewa hanya daya tilo da za su iya zuwa wurin su ita ce idan masu kada kuri’a a rumfunan zaɓe sun samar musu da motocin da za su yi jigilarsu.
Ya zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, lananan motocin bas guda uku ne kawai aka gani a wajen don jigilar jami'an zaɓe sama da 200.
Bam ya fashe kusa da ofishin INEC a Bayelsa
Yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen zaben a Bayelsa, bam ya fashe kusa da ofishin INEC a birnin Yenagoa.
Arise TV ta tattaro cewa an nada wasu ababan fashewa a wurare biyu dabam.
Za a fara zabe misalin karfe 8.30 na safe
Masu zabe sun iso rumfunan zabe a jihohin uku da za a gudanar da zaben yayin da jami'an INEC ke shirya kayan zabe.
Ana sa ran fara zaben misalin karfe 8.30 na safe.
Ma'aikatan INEC sun fara isa rumfunan zaɓe
Ma'aikatan hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC sun fara isa rumfunan zaɓe a jihohin Imo, Kogi da Bayelsa domin gudanar da zaɓen gwamna yau Asabar.
Tuni dai aka raba kayayyakin zaɓe a cibiyoyin kananan hukumomin jihohin uku yayin da ma'aikatan wucin gadi suka durfafi rumfunan zaben da aka tura su suyi aiki.
Channels tv ta tattaro cewa dubbannin ma'aikatan wucin gadi INEC ta ɗauka domin gudanar da zaɓukan jihohin yau 11 ga watan Nuwamba, 2023.
A halin yanzu ana tsammanin fara tantance masu kaɗa kuri'a da jefa ƙuri'a nan bada daɗewa ba.
Zaben Gwamnan Bayelsa na 2023: Manyan yan takara
Alkalluman da INEC ta fitar sun nuna yan takara da jam'iyyun siyasa 16 ne za su fafata a zaben gwamna na Bayelsa. Sai dai, biyar da aka jero a kasa sune ake yi wa kallon manyan yan takara.
- Douye Diri (PDP)
- Timipre Sylva (APC)
- Udengs Eradiri (Labour Party)
- Waibodei Subiri (APGA)
- Warmate Jones (Accord Party)
Zaben Gwamnan Imo na 2023: Manyan yan takara
Alkalluman da INEC ta fitar sun nuna yan takara da jam'iyyun siyasa 17 ne za su fafata a zaben gwamna na Imo. Sai dai, biyar da aka jero a kasa sune ake yi wa kallon manyan yan takara.
- Hope Uzodimma (APC)
- Samuel Anyanwu (PDP)
- Athan Achonu (Labour Party)
- Tony Ejiogu (APGA)
- Lincoln Jack Ogunewe (AA)
Zaben Gwamnan Jihar Kogi na 2023: Manyan yan takara
Alkalluman da INEC ta fitar sun nuna yan takara da jam'iyyun siyasa 18 ne za su fafata a zaben gwamna na Kogi. Sai dai, biyar da aka jero a kasa sune ake yi wa kallon manyan yan takara.
- Usman Ahmed Ododo (APC)
- Dino Melaye (PDP)
- Muritala Yakubu Ajaka (SDP)
- Leke Abejide (ADC)
- Usman Jibrin (Accord Party)
Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng
Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164