Rivers: 'Ban Aikata Laifin da Zai Sa a Tsige Ni Ba', Fubara Ya Yi Martani Kan Yunkurin Kifar Da Shi

Rivers: 'Ban Aikata Laifin da Zai Sa a Tsige Ni Ba', Fubara Ya Yi Martani Kan Yunkurin Kifar Da Shi

  • Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya yi bayanin gaskiyar abin da ke faruwa yayin da ake shirin tsige shi daga mukamin gwamna
  • Fubara ya fuskanci barazanar tsigewa a yau Litinin yayin da majalisar ta cire shugaban ma su rinjaye, Edison Ehie a dakin majalisar
  • Gwamnan ya yi wa ‘yan jihar magana yayin da ya ke bayyana cewa babu wani abu da ya aikata da ya cancanci a tsige shi a kujerar

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ribas - Gwamna Siminalayi Fubara ya bayyana cewa babu abin da ya aikata da ya cancanci tsigewa daga kujerar gwamna.

Fubara ya bayyana haka ne a yau Litinin 30 ga watan Oktoba yayin da aka yi kokarin tsige shi a majalisar dokokin jihar, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen gwamnoni da suka yi wa iyayen gidansu a siyasa karan-tsaye

Fubara ya bayyana cewa bai aikata laifin da za a tsige shi a kujerarshi ba
Fubara Ya Yi Martani Kan Yunkurin Tsige Shi. Hoto: Sir Siminalayi Fubara.
Asali: Facebook

Meye ake shirin yi wa Fubara?

Wannan na zuwa ne yayin da wasu daga cikin mambobin majalisar su ka yi kokarin tsige gwamnan a yau Litinin 30 ga watan Oktoba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da ya ke martani Fubara ya ce:

“Bari na fito na yi wa mutanen jihar Ribas bayani, babu abin da na aikata da na cancanci wannan tsigewa.

Wannan na zuwa yayin da majalisar ta cire shugaban ma su rinjaye, Edison Ehie inda kuma ta yi kokarin hadawa da gwamnan jihar a dakin majalisar, cewar Channels TV.

Gwamna Fubara ya yi jawabi ga 'yan jihar a bakin majalisar jihar a yau Litinin 30 ga watan Oktoba inda ya musu alkawarin romon dimukradiyya.

Meye Fubara ke cewa kan shirin tsigeshi?

Ya kara dacewa:

"Bari in kara ba ku tabbaci ya ku mutanen jihar Ribas, zan ci gaba da samar da romon dimukradiyya, zan yi bayani a lokacin da ya dace ga manema labarai.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari ya hango abin da zai faru idan Majalisa ta tsige Gwamnan Ribas

Wannan na zuwa bayan zargin cewa ministan Abuja, Nyesom Wike ya fara samun matsala da Fubara watanni shida kacal da hawa mulkin jihar.

Ana zargin cewa Wike na ci gaba da juya akalar gwamnatin jihar tun bayan mika mulki da ya yi a watan Mayu.

Majalisa ta mika takardar tsige Fubara

A wani labarin, majalisar jihar Ribas ta shirya tsige Gwamna Fubara bayan ta mika ma sa takardar shirin tsige shi.

Wannan ma zuwa bayan majalisar ta yi yunkurin tsige gwamnan a yau Litinin 30 ga watan Oktoba a fadar majalisar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel