Tinubu: "Ban Yi Dana Sanin Goyon Bayan Shugaban Ba”, Wike Ya Fadi Abu Daya Tak da Zai Yi a 2027

Tinubu: "Ban Yi Dana Sanin Goyon Bayan Shugaban Ba”, Wike Ya Fadi Abu Daya Tak da Zai Yi a 2027

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa bai yi dana sanin nuna goyon baya ga Bola Tinubu ba a zaben da aka gudanar
  • Wike ya ce shi ba dan jam’iyyar APC ba ne amma goyon bayan Tinubu ya zama dole a gare shi saboda babu wanda zai iya kayar da shi a Kudanci
  • Ya bayyana cewa ya sani akwai wadanda ‘yan jam’iyyar APC ne da ba su goyi bayan Tinubu ba amma ya roke su da a hada kai

FCT, Abuja – Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa bai taba dana sanin nuna goyon baya ga Shugaba Tinubu a zaben 2023 ba.

Wike ya bayyana haka ne yayin da karbi bakwancin shugabannin jam’iyyar APC daga jihar Ribas a yau Alhamis 26 ga watan Oktoba, The Nation ta tattaro.

Kara karanta wannan

Shari’ar Zabe: “Ku Yi Hakuri Zuwa 2031”, Ganduje Ya Tura Muhimmin Sako Ga Atiku, Obi

Wike ya ce bai taba dana sanin nuna goyon baya ga Tinubu ba a 2023
Wike ya yi martani kan goyon bayanshi ga Tinubu. Hoto: Bola Tinubu, Nyesom Wike.
Asali: Facebook

Meye Wike ke cewa kan Tinubu?

Ministan ya sha alwashin marawa Shugaba Tinubu baya a zaben 2027 wurin nema masa kuri’u a wurin al’umma, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce bai yi dana sanin goyon bayan Tinubu ba saboda ya fito ne don nema wa mutane adalci don haka babu wanda ya ke bin shi bashin neman afuwa.

Ya yi alkwarin tafiya da kowa ba tare da bambancin addini ko yare ko kuma siyasa ba, inda ya ce zai tafi tare da jam’iyyar APC da ‘yan Najeriya baki daya.

Wane shawara ya bai wa APC kan Tinubu?

Ya ce:

“Nagode wa Allah yau shari’ar ta kare, dukkanmu ‘yan Najeriya ne ya kamata mugane cewa Najeriya ta mu ce gaba daya ba ta wani ba.
“Ba zan nuna wariya ga kowa ba ta bangaren addini ko siyasa ko kuma yare, ni na kowa ne, ina tare da kowa har ma da wadanda ba ‘yan jam’iyyarmu ba.

Kara karanta wannan

"A Hankali Mu Na Rikidewa Zuwa Lalatacciyar Jam'iyar PDP", Jigon APC Ya Soki Tsarin Shugabancin Jam'iyyar

“Shugaban kasa ya yi nasara, ba shugaban APC ba ne, shugaban Najeriya ne gaba daya, yayin da ya ke mulki dole zai kare muradun jam’iyyarsa, babu mai yin musun haka.”

Wike ya ce shi ba dan APC ba ne amma goyon bayan Tinubu ya zama dole a gare shi, ganin yadda dukkan Kudanci babu wanda zai kayar da Tinubu.

Wike ya yi martani kan zargin kin Musulunci

Kun ji cewa, ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa ko kadan ba ya gaba da Musulunci.

Wike ya bayyana haka ne yayin da ake zargin ya shirya rushe wani bangaren masallacin Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel