Rikicin PDP: Gwamnonin G-5 Sun Sake Haduwa a Abuja, Sun Gana da Shugaba Tinubu

Rikicin PDP: Gwamnonin G-5 Sun Sake Haduwa a Abuja, Sun Gana da Shugaba Tinubu

  • Gwamnonin G-5 na jam'iyyar PDP sun sake haɗa kansu, sun gana da shugaba Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja
  • Rahoto ya nuna tawagar G-5 wacce ta ƙunshi tsoffin gwamnoni 4 da gwamna mai ci, sun fara zama tsakaninsu a gidan Ministan Abuja
  • Duk da babu cikakken bayani kan abinda suka tattauna, amma ana ganin ba zai rasa nasaba da alaƙarsu ta aiki ba

FCT Abuja - Tawagar gwamnonin jam'iyyar PDP 5 karkashin jagorancin Nyesom Wike, Ministan babban birnin tarayya Abuja sun sake haɗa kansu sun gana a gidan Wike.

Gwamnonin G-5 dai sun ƙunshi tsoffin gwamnonin PDP guda huɗu da kuma gwamna mai ci guda ɗaya, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Gwamnonin G5 sun sake zama da shugaba Tinubu.
Rikicin PDP: Gwamnonin G-5 Sun Sake Haduwa a Abuja, Sun Gana da Shugaba Tinubu Hoto: @Topboychriss
Asali: Twitter

Tawagar G-5 ta gana da shugaba Tinubu

An tattaro cewa gwamnonin G-5 sun gana da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a fadarsa da ke Abuja jim kaɗan bayan kammala taronsu a gidan Wike.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Jihar APC Ta Yi Magana Kan Batun Sake Fitar da Gwamna Mara Lafiya Kasar Waje Domin Jinya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan Abuja ne ya jagorance su zuwa wurin shugaba Tinubu, sai dai har yanzu ba bu cikakkun bayanai kan batutuwan da suka tattauna da shugaban ƙasa.

Amma wasu rahotanni sun nuna cewa taron ya maida hankali ne kan alaƙa ta aiki da ta haɗa shugaba Tinubu da gwamnonin G-5 na PDP wanda ya samo asali tun kafin zaɓen 2023.

Wata majiya a taron wanda ta nemi a sakaya sunanta saboda ba ta da izinin yin magana kan batun ta ce:

"A farko Gwamnonin PDP na G-5 sun gana a gidan Wike na ‘yan sa’o’i kafin daga bisani su wuce Villa domin ganawa da shugaban ƙasa. Ba ni da cikakken bayani game da abin da aka tattauna a halin yanzu."
"Amma daga tattaunawar da aka yi a lokacin taron farko da aka yi a gidan Wike, ya shafi nemo matsuguni ga tsofaffin gwamnonin da kuma yadda za su ci gaba da aiki tare."

Kara karanta wannan

Gwammatin Tinubu Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Mutane Aikin N-Power Na 2023? Gaskiya Ta Bayyana

Gwamna da tsoffin gwamnonin da suka halarci zaman

Tsoffin gwamnonin da suka halarci zaman sun haɗa da Nyesom Wike na Ribas, Samuel Ortom na Benuwai, Ifianyi Ugwuanyi, na Enugu da kuma Okezie Ikpeazu na Abiya.

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ne kaɗai gwamnan da ke kan madafun iko kuma ya halarci taron ranar Talata, The Angle ta tattaro.

Majalisar Dattawa Ta Shiga Zaman Sirri Bayan Ndume Ya Soki Sanata Akpabio

A wani rahoton kuma rigima na neman ɓarke wa a majalisar dattawa yayin da aka ga Sanata Ndume ya tattara kaya ya fice daga zauren majalisar.

Sanatan ya fara da korafin cewa yanayin yadda ake tafiyar da harkokin majalisar ya saɓa doka amma Akpabio ya hana shi ƙarisa wa, lamarin da ya fusata shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel