Gwammati Ta Buɗe Shafin Daukar Sabbin Ma'aikatan N-Power? Gaskiya Ta Bayyana

Gwammati Ta Buɗe Shafin Daukar Sabbin Ma'aikatan N-Power? Gaskiya Ta Bayyana

  • Tsarin N-Power da gwamnatin jam'iyyar APC ta kirkiro bayan hawa mulki a 2015 na ɗaya daga cikin manyan nasarorin da ta samu
  • Legit Hausa ta gano cewa tun da aka kaddamar da shirin N-Power a 2016, an ɗauki rukuni uku wanda ya ƙunshi matasa kusan miliyan guda
  • Gabanin gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin a watan Oktoba, wani rahoto ya yi ikirarin an buɗe shafin ɗaukar sabbin mutane na 2023

FCT Abuja - Wani rahoto da aka wallafa a dandalin sada zumunta Facebook ya yi ikirarin cewa an bude shafin yanar gizo domin cike aikin N-Power 2023.

A cewar rubutun da aka wallafa, duk matasan 'yan Najeriya da ke sha'awar "zama masu cin gajiya" a tsarin zasu iya cike Fam a Fotal ɗin yanar gizo-gizo.

Gwamnati ba ta buɗe shafin cike neman aikin Npwer ba.
Gwammati Ta Buɗe Shafin Daukar Sabbin Ma'aikatan N-Power? Gaskiya Ta Bayyana Hoto: Npower
Asali: Facebook

N-Power: Ku guji faɗawa shafin 'yan damfara

Kara karanta wannan

Ministan Birnin Tarayya Nyesom Wike Ya Bayyana Dalilin da Yasa Ya Yarda Ya Yi Aiki da Tinubu

Rahoton wanda NGCareers ta wallafa ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta, 2023, ya ja hankalin mutane sama da 2,700, aƙalla mutum 1,000 suka yi sharhi, 32 kuma suka tura wa abokansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A martanin da Legit Hausa ta gani, da yawan waɗanda suka yi sharhi kan rahoton sun nuna sha'awar shiga tsarin na N-Power.

Shin wannan labari na gaskiya ne? Legit Hausa ta yi bincike

Legit Hausa ta latsa adireshin shafin yanar gizon da aka haɗa a rahoton kuma ya kaimu zuwa wani Fortal wanda bai da tsaro kuma ba shi da alaƙa da gwamnati.

Daga nan kuma mun latsa wurin da aka sa "Apply Here" wato cike Fam ɗin nuna sha'awa domin ganin kwakwaf, inda ya nuna mana Fam da aka nemi mu cike suna, Email, jinsi, jiha da lambar waya.

Da farko dai adireshin yanar gizon ba shi da "gov.ng" wanda ke nuna na gwamnatin tarayya ne.

Kara karanta wannan

'Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Tsallake Rijiya da Baya Yayin da Aka Kai Masa Harin Kisa Sau 4 a Arewa

Kuma bayan cika cikakkun bayanan da ake buƙata, sai ya kaimu shafin yanar gizon wanda ke bayanin yadda ake neman gurbi a Jami'ar Harvard da ke ƙasar Amurka.

Shafin na ƙarya ne

Daga ƙarshe dai babu wata sanarwar fara cike aikin N-Power daga shafukan sadarwa na gwamnatin tarayya. Legit Hausa ta bi shafukan ma'aikatun jin ƙai, yaɗa labarai da wayar da kai amma ba ta ga komai ba.

Baya ga haka, karo na karshe da FG ta dauki aikin N-Power shi ne a shekarar 2022, inda gwamnati ta ɗauki karin matasa cikin shirin.

Sanata Ya Tona Asirin Gwamnan APC Na Arewa Dake Ƙokarin Zarce Wa Zango Na Uku

A wani rahoton na daban Sanata Dino Melaye ya bayyana ƙwarin guiwar cewa shi zai lashe zaɓe gwamnan jihar Kogi a zaɓen ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.

Melaye ya ce Gwamna Yahaya Bello na amfani da Usman Ododo, ɗan takarar gwamna a inuwar APC domin ya ci gaba da mulki karo na uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel