Kashim Shettima Ya Ce Najeriya Na Bukatar Naira Tiriliyan 21 Don Magance Matsalar Ƙarancin Gidaje

Kashim Shettima Ya Ce Najeriya Na Bukatar Naira Tiriliyan 21 Don Magance Matsalar Ƙarancin Gidaje

  • Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya yi tsokaci kan ƙarancin gidajen da ake fama da su a Najeriya
  • Ya ce a yanzu haka ana bukatar naira tiriliyan 21 don shawo kan matsalar a fadin Najeriya
  • Ya bayyana hakan ne wajen ƙaddamar da ginin rukunin gidaje 500 da gwamnatin Sokoto ta yi

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa duk da ƙoƙarin da gwamnatoci a duka matakai suke yi wajen magance matsalolin ƙarancin gidaje, har yanzu ana bukatar naira tiriliyan 21.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne ranar Lahadi a Sokoto, a wajen ƙaddamar da ginin rukunin gidaje 500 da gwamnatin jihar ta yi kamar yadda aka wallafa a shafin Gwamnatin Tarayya.

Shettima ya fadi kuɗaɗen da Najeriya take buƙata don magance matsalolin karancin gidaje
Kashim Shettima ya ce Najeriya na bukatar naira tiriliyan 21 don magance matsalolin karancin gidaje. Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Najeriya na bukatar tiriliyan 21 saboda karancin gidaje

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Ta Samo Rancen Dala Miliyan 163 Domin Yin Wani Muhimmin Abu 1

Kashim Shettima ya jinjinawa gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu bisa ƙoƙarin da yake na magance matsalolin karancin gidajen da mutanensa ke fuskanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce wannan matakin da ya ɗauka mataki ne mai kyau wajen magance matsalolin al'ummarsa abu ne mai kyau da ya kamata sauran gwamnonin jihohi su yi koyi da shi.

Shettima ya kuma bayyana cewa a yanzu haka Najeriya na bukatar karin gidaje miliyan 28, wanda hakan zai laƙume aƙalla naira miliyan 21.

Mutanen da za su ci gajiyar gidajen da aka gina

Da yake jawabi a wajen taron ƙaddamar da gine-ginen, Gwamna Aliyu ya bayyana cewa za a sayarwa da gidajen da za a gina ne ga ma'ikatan gwamnatin jihar ta Sokoto.

Ya ce tun lokacin tsohon gwamnan jihar Aliyu Magatakarda Wamakko aka fara aikin, sai dai gwamnatin da ta shuɗe ta yi watsi da shirin a lokacinta, wanda yakan ne ya sa suka dawo da shi domin amfanin al'ummar jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnoni Jihohin Arewa Sun Cimma Matsaya, Sun Gaya Wa Jami'an Tsaro Abinda Yakamata Su Yi Kan Matsalar Tsaro

Ya ƙara da cewa gine-ginen waɗanda ake yinsu yanzu haka a yankin ƙaramar hukumar Wamakko, za su laƙume kuɗaɗen da yawansu ya kai naira biliyan bakwai da ɗigo uku kamar yadda Channels TV ta wallafa.

Gwamnatin Tinubu ta karbo rancen dala miliyan 163

Legit Hausa a baya ta yi rahoto kan rancen dala miliyan 163 da gwamnatin Tinubu ta karɓo domin bunƙasa noma alkama a ƙasa baki ɗaya.

Shettima ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ta sha alwashin cika duka alƙawuran da ta ɗauka musamman ma dai na bangaren noma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel