Gwamnatin Tarayya Ta Karbo Rancen Dala Miliyan 163 Don Bunkasa Noman Alkama

Gwamnatin Tarayya Ta Karbo Rancen Dala Miliyan 163 Don Bunkasa Noman Alkama

  • Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya bayyana shirin Gwamnatin Tarayya na samar da abinci
  • Ya ce yanzu haka gwamnatin ta karɓo rancen dala miliyan 163 don bunkasa noman alkama
  • Shettima ya kuma bayyana cewa gwamnatin Tinubu za ta cika duka alƙawuran da ta ɗaukarwa manoma

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Argungu, jihar Kebbi - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana cewa ta samu rancen kuɗaɗe har dala miliyan 163 daga bankin raya nahiyar Afrika (AfDB), domin bunƙasa noman alkama.

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a fadar mai martaba sarkin Argungu Alhaji Sumaila Mohammed kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Shettima ya ce sun karbo rancen dala miliyan 163 don bunkasa noman alkama
Gwamnatin Tarayya ta samu rancen kuɗaɗe har dala miliyan 163 domin bunƙasa noman alkama. Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Najeriya ta karbo dala miliyan 163 daga bankin AfDB

Shettima dai ya je Argungu ne domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu wajen ta'aziyyar fitaccen malamin addinin Musulunci Sheikh Giro Argungu da ya rasu a makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima Ya Bayyana Yankunan Da Za Su Ci Gajiyar Mulkin Shugaba Tinubu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana cewa yanzu haka gwamnati ta riga da ta amso bashin dala miliyan 163 daga bankin na AfDB, kuma nan ba da jimawa ba za a kaddamar da shirin haɓaka noman na alkama.

Shettima ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta cika duk alƙawuran da ta ɗauka musamman ma a bangaren noma domin samar da abinci.

Shettima ya taya iyalan Sheikh Giro jimamin rasuwarsa

A yayin da ya ziyarci gidan marigayi Giro Argungu, Shettima ya bayyana cewa Najeriya da ma Afrika baki ɗaya sun yi babban rashi na fitaccen malamin addinin Musulunci.

Ya ce Sheikh Giro malami ne da ya yi wa addini hidima domin Allah ba wai don wani abin duniya da zai samu ba kamar yadda jaridar Leadership ta wallafa.

Kara karanta wannan

"Kowace Jiha 1,000" Shugaba Tinubu Ya Amince da Muhimmin Aiki a Jihohi 7 Na Arewacin Najeriya

Ya ƙara da cewa Shugaba Bola Tinubu ne ya umarce shi da ya taso zuwa jihar Kebbi domin yin ta'aziyyar fitaccen malamin da aka rasa.

Shugaban kungiyar Izala na ƙasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau a madadin iyakan Sheikh Giro, ya godewa shugaban kasa da mataimakinsa bisa nuna kulawarsu akan iyalan malamin.

Shettima ya bai wa 'yan Najeriya haƙuri kan halin da ake ciki

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan haƙurin da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya bai wa 'yan Najeriya kan halin ƙuncin rayuwar da ake ciki.

Shettima ya bayyana cewa gwamnati na yin iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin kowane yankin na ƙasar nan ya amfana da romon dimokuraɗiyyar da take shirin rabawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel