Gwamna Babagana Umara Zulum ya bude sabbin gidaje 50 da ya ginawa kananan malaman jami'ar UNIMAID

Gwamna Babagana Umara Zulum ya bude sabbin gidaje 50 da ya ginawa kananan malaman jami'ar UNIMAID

- Bayan ginawa manyan ma'aikata gidaje 20, gwamna Zulum ya sake gwangwaje kananan malamai

- Zulum ya gina wadannan gidaje cikin watanni 11 kacal

- Ya bada umurnin samar da shiri da zai baiwa ma'aikatan jami'ar daman mallakar gidajen kansu

Gwamnan Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya kaddamar da gidaje 50 da gwamnatin jihar ta gina domin jin dadin kananan ma'aikatan jami'ar Maiduguri.

An fara wannan ginin ne a watan Disamban 2019 kuma yana cikin ayyukan da gwamna Zulum ke yi domin jin dadin yan asaliin jihar Borno.

Wannan shine jerin gidaje na biyu da da gwamna Zulum ya ginawa manyan ma'aikatan jami'ar Maiduguri.

A Disamban 2019, ya kaddamar da gidaje 20 da ya ginawa manyan ma'aikatan jami'ar.

A bikin bude gidajen, Zulum ya bada umurnin biyan malaman jami'a da rikicin gwamnatin tarayya da ASUU ya shafa wasu kudade don rage radadi.

KU KARANTA: Gwamnatin jihar Kaduna ta dakatad da shugaban kwamitin zaben sarki, Wazirin Zazzau

Gwamna Zulum ya umurci Sakataren gwamnatin jihar ya hada kai da bankin jihar wajen samar da wani shirin da zai tabbatar da cewa kananan ma'aikatan jami'ar sun mallaki gidajen kansu.

Bugu da kari, gwamnan ya bada umurnin sake gina tsangayar koyar da ilimin Injiniyanci kuma ya yi umurnin sayan kayayyakin da ake bukata wajen inganta sashen ilimin injiyancin gine-gine.

Bayan haka, Zulum ya yi kira ga ASUU su duba halin da jihar Borno ke ciki su sassauta yajin aikin da sukeyi.

Gwamna Babagana Umara Zulum ya bude sabbin gidaje 50 da ya ginawa kananan malaman jami'ar UNIMAID
Gwamna Babagana Umara Zulum ya bude sabbin gidaje 50 da ya ginawa kananan malaman jami'ar UNIMAID Hoto: GovZulum
Asali: Facebook

KU KARANTA: Kakakin majalisar wakilai ya tona asirin dan sandan da ya bindige mai jarida a Abuja

Gwamna Babagana Umara Zulum ya bude sabbin gidaje 50 da ya ginawa kananan malaman jami'ar UNIMAID
Gwamna Babagana Umara Zulum ya bude sabbin gidaje 50 da ya ginawa kananan malaman jami'ar UNIMAID Hoto:GovZulum
Asali: Facebook

A bangare guda, bayan watanni 8 ana muhawara, gwamnatin tarayya ta amince da bukatun kungiyar malaman jami'a ASUU cewa a togaciye mambobinta daga manhajar biyan albashi ta IPPIS.

A zaman da gwamnatin tayi da shugabannin ASUU ranar Juma'a, ta hakura kan wasu lamura wanda ya hada da wajabta biyan malaman ta IPPIS da kuma kar musu kudin alawus da kudin gyaran jami'o'i.

Yayin karanto abubuwan da suka tattauna bayan sa'o'i bakwai ana tattaunawa a dakin taron ma'aikatar kwadago, Ministan, Chris Ngige, ya ce gwamnati ta amince a biya mambobin ASUU albashinsu tun daga watan Febrairu zuwa Yuni da tsohon manhajar GIFMIS.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel