Kotun Zabe: Manyan Dalilai 5 Da Ka Iya Sa a Tsige Tinubu a Matsayin Shugaban Kasar Najeriya

Kotun Zabe: Manyan Dalilai 5 Da Ka Iya Sa a Tsige Tinubu a Matsayin Shugaban Kasar Najeriya

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na gab da sanin makomarsa yayin da kotun zaben shugaban kasa ke a matakin karshe
  • An gabatar da korafe-korafe da shaidu da dama a gaban kotun zaben yayin da yan kasa ke kallon kwamitin mai mutum biyar da ke da alhakin tabbatar da damokradiyyar Najeriya
  • Paul Ibe, mai ba dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP shawara kan harkokin labarai, ya shaidawa Legit.ng cewa, shaidun da ke gaban kotu sun isa a yi adalci

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Yayin da kotun zaben shugaban kasa ta kai matakin karshe, kallo ya koma kan kamitin mutum biyar na kotun daukaka karar domin yanke hukuncin karshe bayan gabatar da shaidu da dama, sauraron shaidu da kuma hujjojin masu kara.

Sai dai kuma, Yan Najeriya na cikin shirin ko-ta-kwana, cike da fargaba amma dai sun saurara suna jiran hukunci kan shari’ar da ta fi kowacce muhimmanci a tarihin dimokradiyyar Najeriya.

Kara karanta wannan

Jigon APC Ya Yi Garaje, Ya Fadi Wanda Zai Yi Nasara a Kotun Karar Zaben 2023

Kotun zabe za ta yanke hukunci inda Tinubu zai san makomarsa a matsayin shugaban kasar Najeriya
Kotun Zabe: Manyan Dalilai 5 Da Ka Iya Sa a Tsige Tinubu a Matsayin Shugaban Kasar Najeriya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A daya bangaren kuma, ba za a iya hasashen ga abun da zai faru da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba, sakamakon kararraki daban-daban da aka shigar a kansa da kuma hujjojin da aka gabatar a gaban kotun zaben shugaban kasa.

Sai dai har yanzu ba a ba shi tabbacin kujerarsa a Aso Rock a matsayin zarge-zargen da ake yi masa ba, kuma shaidun na iya zama muhimmi ga hukuncin karshe da kotun za ta yanke.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wannan zauren, Legit.ng ta lissafo wasu manyan abubuwa biyar da ka iya sa Tinubu ya rasa kujerarsa.

1. Rashin gudanar da zabe mai inganci

Wannan dai batu ne da aka shafe watanni ana yi tun bayan kammala zaben shugaban kasar.

Masana harkokin siyasa da dama da masu sharhi kan al'amuran jama'a na ta caccakar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) kan yadda ta gudanar da zaben shugaban kasar.

Kara karanta wannan

An Baza Jami’an Tsaro Kafin Tinubu, Atiku, Obi Za Su San Makomarsu a Kotu

A baya-bayan nan ne tawagar masu sa ido kan zabuka ta Tarayyar Turai ta fitar da wani rahoto da ke nuna cewa zaben bai da inganci da sahihanci.

Rahoton ya kuma bayyana cewa ana shakku a kan sahihancin jami’an hukumar INEC da shugabanninta.

Hakazalika, mai ba dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP shawara kan harkokin labarai, Paul Ibe, ya shaidawa Legit.ng cewa shaidun da aka gabatar a gaban kotun sun kuma lissafa tare da bayyana rashin gamsuwa da rashin gaskiyar INEC.

“Alkalan kotun daukaka kara sun duba dukkan hujjoji, kuma na yi imanin za su yi adalci a kan hujjojin da suka nuna cewa an tafka magudi a zaben, cewa zaben bai yi daidai da dokar zabe da tsarin gudanarwar INEC ba."

2. Zargin safarar miyagun kwayoyi

Wannan lamari ne da Shugaban kasa Tinubu ya dade yana fama da shi kasancewar Atiku Abubakar da Peter Obi ne suka shigar da kara kansa a gaban kotunzaben.

Kara karanta wannan

Kotun Daukaka Kara Ta Dauki Mataki Yayin da Ake Dab da Yanke Hukunci Kan Nasarar Tinubu a 2023

An tattaro cewa tawagar lauyoyin Tinubu ta yarda a kotun zaben cewa wanda suke karewa ya taba bayar da dala 460,000 ga gwamnatin Amurka kan laifin safarar miyagun kwayoyi da kuma wawure kudade.

A jawabin karshe da Atiku ya yi, an bayyana karara cewa saboda amsa wannan laifi da ya yi, Tinubu bai:

"Hurumin tsayawa takarar shugaban kasar Najeriya, balle har a ayyana shi a matsayin shugaban kasar Najeriya."

3. Katin dan kasa guda biyu

Daga cikin karar da Atiku ya shigar da shaidun da aka gabatar gaban kotun zaben, an zargi Shugaban kasa Tinubu da mallakar fasfot din kasar Guinea.

Wani rahoto da Legit.ng ta samu a baya ya nuna cewa kungiyar lauyoyin shugaba Tinubu ta amince cewa ya mallaki fasfo din wata kasa.

Sai dai kuma, hujjar da suka gabatar a gaban kotu, ta bayyana cewa shugaban kasa Tinubu ya soke katin dan kasar tun a shekarar 2020.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Rantsar da Sabbin Shugabannin Kananan Hukumomi 18 da Suka Lashe Zaɓe a Jiharsa

Korafe-korafen da aka shigar a gaban kotun sun nuna cewa hakan cin zarafin dokar zabe ne da ya kamata a yi la'akari da shi wajen hana shi shiga takara.

4. Juyin mulkin Nijar da fafutukar ECOWAS

Alamu sun nuna Tinubu, wanda shine shugaban ECOWAS a yanzu haka, yana fuskantar matsala wajen ba da umarni a yankin biyo bayan juyin mulkin Nijar.

Tinubu ya yi umurnin mayar da mulki ga farar hula cikin kwanaki bakwai, amma shugaban sojin juyin mulki a Nijar ya ce ba zai ba da hadin kai ba.

Wani gidan talbijin na Afirka ta Kudu ma ya yi nazari a kan cewa nasarar da Tinubu ya samu a zaben shugaban kasa na da nasaba da raunin ikonsa a matakin kananan hukumomi.

Shugabannin sojojin Mali da na Burkina Faso sun gargadi Shugaba Tinubu kan tsoma baki cikin harkokin Nijar.

5. Atiku ya lashe jihohi 21 kamar yadda INEC ta sanar

Kara karanta wannan

A Karon Farko, Tinubu Ya Yi Martani Game Da Shari'ar Zabe Tun Bayan Saka Ranar Hukunci, Ya Ce Ko A Jikinsa

Wannan wani muhimmin lamari ne da Atiku da PDP suka ci gaba da matsawa kotun zaben a kansa don ta yanke hukunci.

Kamar yadda yake kunshe a cikin jawabin karshe na Atiku, ta hannun lauyansa, Chris Uche SAN, ya bayyana cewa har yanzu lamarin bai samu wani cikas a cikin shari'ar da ake gudanarwa ba.

Ana hasashen wannan zai zama muhimmi abu a hukuncin karshe da kotun za ta yanke.

Babbar Malamar Addini Ta Bayyana Zabin Allah a Tsakanin Atiku, Tinubu da Peter Obi

A wani labarin, mun ji cewa Fasto Christiana Eunice, wacce ta kafa cocin Covenant Of God Church Praise Sacrament, a ranar Talata, 5 ga watan Satumba, ta bayyana cewa Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), shi ne zaɓin Allah.

A yayin da take magana a WomanOfGod TV, fasto Eunice ta bayyana cewa gwamnatin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), kallon da ƴan Najeriya su ke mata ba haka take ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel