Shari’ar Zabe: Dalilai 3 Da Suka Sa Kotu Ta Yi Fatali Da Karar Da APM Ta Shigar Kan Tinubu Da Shettima

Shari’ar Zabe: Dalilai 3 Da Suka Sa Kotu Ta Yi Fatali Da Karar Da APM Ta Shigar Kan Tinubu Da Shettima

  • An kori karar da jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM) ta shigar a kan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima
  • An tattaro cewa kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta kori karar kan dalilai uku
  • An rahoto cewa an yanke hukunci kan karar da APM ta shigar a kotun koli don haka kotun zaben ta ce bata da hurumin sauraronta

Abuja - Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta kori karar da jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM) ta shigar a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba.

An tattaro cewa karar ta nemi a soke zaben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima.

Kotun zabe ta kori karar APM kan Tinubu da Shettima
Shari’ar Zabe: Dalilai 3 Da Suka Sa Kotu Ta Yi Fatali Da Karar Da APM Ta Shigar Kan Tinubu Da Shettima Hoto: Bola Ahmed Tinubu/APM
Asali: Facebook

Kamar yadda Legit.ng ta tattaro, kotun zaben ta soki karar da suka shigar akan wasu dalilai guda uku.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Yi Hukunci Kan Karar Peter Obi Na Zargin Tinubu Kan Safarar Kwayoyi A Amurka

1. Rashin hurumi

An tattaro cewa kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta yi fatali da karar da APM ta shigar, saboda bata da hurumi a shari'ar, saboda ya shafi wani abu da ya faru kafin zabe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na nufi cewa ya kamata ace an saurari karar ne a wani mataki na daban.

Akwai kuma yiwuwar cewa jam'iyyar APM na iya daukaka kara a matakin kotun Allah ya isa.

2. Rashin cancantuwar shigar da karar

Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasar ta ce mai karar bata cancanci shigar da karar da ta kai gaban kotu ba.

3. Hukuncin Kotun Koli

Kotun zaben ta lura cewa Kotun Koli ta riga ta yanke hukunci, wanda hakan ba zai ba da damar sake zama a kan lamarin ba, tana mai nuni ga cewa an riga an yanke hukunci.

Kara karanta wannan

Muhimman Dalilai 5 Da Zasu Iya Sa Kotun Zabe Ta Tsige Shugaba Tinubu Daga Kujerar Mulkin Najeriya

Da yake ci gaba da karin haske kan lamarin, Bulama Burkati, wani lauya, ya bayyana a manhajar X cewa:

"Kowani daya daga cikin wadannan dalilai, bisa ga ka'idojin shari'a, zai iya sa karar APM ya zama wanda bai dace ba. Sai dai duk da wannan tangardar, Kotun ta ci gaba da duba cancantar karar."

Bayan ta yi nazari sosai a kan duk wasu kararraki, shaidu, da kuma gardama, Kotun ta yanke hukuncin cewa karar bata cancanta ba.

A karshe ta cee sabanin ikirarin APM, ba a tsayar da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima sau biyu ba, saboda ya janye takararsa na Sanatan Borno.

Bugu da kari, ta ce shugaba Bola Tinubu na da yancin zabar abokin takararsa, matukar dai an yi wannan zaben cikin wa’adin da doka ta tanada.

Dalilai 5 da ka iya sa kotu ta tsige shugaban kasa Tinubu

A gefe guda, mun ji cewa yayin da kotun zaben shugaban kasa ta kai matakin karshe, kallo ya koma kan kamitin mutum biyar na kotun daukaka karar domin yanke hukuncin karshe bayan gabatar da shaidu da dama, sauraron shaidu da kuma hujjojin masu kara.

Sai dai kuma, Yan Najeriya na cikin shirin ko-ta-kwana, cike da fargaba amma dai sun saurara suna jiran hukunci kan shari’ar da ta fi kowacce muhimmanci a tarihin dimokradiyyar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel