Ibadan: 'Yan Fashi Sun Kai Farmaki Babban Birnin Jihar Oyo, Sun Tafka Ta'asa

Ibadan: 'Yan Fashi Sun Kai Farmaki Babban Birnin Jihar Oyo, Sun Tafka Ta'asa

  • Wasu miyagun 'yan fashi da makami sun kai farmaki yankuna uku a Ibadan, babban birnin jihar Oyo da sanyin safiyar Talata
  • Wani shugaban al'umma a ɗaya daga cikin yankunan da harin ya shafa, ya tabbatar da cewa maharan sun jawo wa mutane asara
  • Har kawo yanzun ba a samu jin ta bakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sanda ba, amma bayanai sun nuna yan fashin sun yi awon gaba da kayayyaki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ibadan, Oyo - Wasu 'yan fashi da Makami sun sai farmaki yankuna uku a Ibadan, babban birnin jihar Oyo da sanyin safiyar ranar Talata, 5 ga watan Satumba, 2023.

Jaridar Punch ta rahoto cewa 'yan fashin sun tafka ta'asa inda suka yi awon gaba da Kuɗaɗe, Wayoyin hannu da Sarƙoƙi da sauran kayayyaki masu muhimmanci.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Tarwatsa Mutanen Garuruwa Sama da 15 Yayin da Suka Kai Mummunan Hari a Jihar Arewa

Yan fashi sun kai farmaki Ibadan.
Ibadan: 'Yan Fashi Sun Kai Farmaki Babban Birnin Jihar Oyo, Sun Tafka Ta'asa Hoto: Oyo
Asali: UGC

Wane yankuna maharan suka kai hari?

Yankunan da wannan hari ya shafa sun haɗa da, Alaja, Seriki, da Ogogo da ke kan sabon babban titun Ibadan/Oyo a ƙaramar hukumar Akinyele.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wakilin jaridar, wanda ya ziyarci yankunan da 'yan fashin suka shiga, ya gano cewa lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 3:00 na dare wayewar garin Talata.

Ɗaya daga cikin shugabannin al'umma, Raji Kazeem, ya yabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Ya ce:

"Eh da gaske ne, 'yan fashi da makamai sun kawo mana hari da tsakar dare kuma sun yi fashi a wasu gidajen jama'a. Wannan ne ya sa mutane suka kasu suna ta magana kan abinda ya auku."

Har kawo yanzu da muke haɗa wannan rahoton, duk wani yunƙurin jin ta bakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda reshen jihar Oyo, Adewale Osifeso, bai kai ga nasara ba.

Kara karanta wannan

Shari'ar Atiku, Obi Da Tinubu: Jami'an Tsaro Sun Fitar Da Muhimmin Gargaɗi Gabanin Yanke Hukunci

Kakakin yan sandan bai ɗaga kiran wayar da aka masa ko turo amsoshin saƙonnin karta kwanan da aka tura ta lambarsa ba har yanzun, kamar yadda rahoton Politics Nigeria ya tabbatar.

Edo: Shaibu Ya Janye Karar da Ya Maka Gwamna Obaseki a Kotu

A wani rahoton na daban alamu sun nuna an fara shawo kan rigimar da ta haɗa mataimakin gwamnan Edo, Philip Shaibu da gwamna Obaseki na PDP.

Mista Shaibu ya bayyana cewa ya janye ƙarar da ya shigar gaban babbar Kotun tarayya inda ya nemi a dakatar da gwamna Obaseki daga yunƙurin tsige shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel