An Baza Jami’an Tsaro a Ko Ina a Abuja, Tinubu, Atiku, Obi Za Su San Makomarsu a Kotu

An Baza Jami’an Tsaro a Ko Ina a Abuja, Tinubu, Atiku, Obi Za Su San Makomarsu a Kotu

Duk inda aka san rigima za ta iya barkewa yau a Abuja, an baza ‘yan sanda da dakarun NSCDC

Motocin ‘yan sanda sun soma yawo tun ranar Talata domin shiryawa zaman kotun shari’ar zaben 2023

A yau Alkalai za su zartar da hukunci a kan karar da PDP, LP da APM ta shigar a kan Bola Tinubu

Abuja - Jami’an tsaro sun cika wuraren da ake ganin za a iya samun hayaniya a sakamakon hukuncin da kotun sauraron karar zabe za tayi a yau.

A yau Laraba ne kotun karar zaben shugaban kasa za ta yanke hukunci tsakanin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da abokan adawarsa a takarar 2023.

Punch ta ce an tura ‘yan sanda, jami’an NSCDC da sauran jami’an tsaro masu fararen kaya domin shiryawa hukuncin da za a zartar yau a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Shari'ar Atiku, Obi Da Tinubu: Jami'an Tsaro Sun Fitar Da Muhimmin Gargaɗi Gabanin Yanke Hukunci

'Yan sanda
'Yan sanda a lokacin zaben 2023 Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a hana aukuwar rikici a kotun zabe

Makasudin tura jami’an tsaron shi ne a tabbatar da rikici bai barke daga magoya baya ba.

Saboda gudun tashin-tashina ne aka bada sanarwa tun kafin yanzu cewa babu wanda zai shiga kotun illa wasu wadanda hukuma ta tantance su.

'Yan sanda su na bakin aiki a Abuja

Wurare irinsu Three Arms Zone, Julius Berger, Area One, Wuse cike su ke da masu damara kamar yadda motoci su ke sintiri kan wasu manyan tituna.

Da kimanin karfe 6:50 na yamma aka ji cewa an shigo da motocin ‘yan sanda zuwa harabar kotun, su ne za su kewaye yankin domin a tabbatar da tsaro.

Sannan an hangi wasu jami’an ‘yan sandan su na sintiri yayin da su ke karbar umarni daga manyansu.

Shari’ar zaben 2023 a Najeriya

Ku na sane Atiku Abubakar, Peter Obi da jam’iyyar APM su na shari’a da Bola Ahmed Tinubu da APC, ba ta gamsu da nasarar da hukumar INEC ta ba shi ba.

Kara karanta wannan

Jerin Kararrakin Zaben Da Aka Gudanar Tun Shekarar 1999 Da Sakamakon Da Aka Samu

Mai shari’a Haruna Tsammani zai gabatar da hukunci tare da sauran Alkalai; Stephen Adah, Monsurat Bolaji-Yusuf, Moses Ugo, da Abba Mohammed.

Jigon PDP ya nemi ayi adalci

A baya an rahoto Cif Olabode George wanda jigo ne a PDP ya na kira ga Alkalai su yi adalci wajen yin hukuncin a kan 'yan takarar shugaban kasar na 2023.

Za ayi zaman karshe ne a kotun daukaka kara da ke birnin Abuja. Daga nan kuma damar da ta rage ita ce kotun koli, bayan nan sai da ayi Allah ya isa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel