Jam’iyyar APC Ta Yi Nade-Naden Mukamai, An Maye Guraben Wadanda Su ka Bar NWC

Jam’iyyar APC Ta Yi Nade-Naden Mukamai, An Maye Guraben Wadanda Su ka Bar NWC

  • Jam’iyyar APC ta gudanar da zabuka da nufin samun sababbin shugabannin da za su rike NWC
  • A makon nan aka samu karin mutane cikin uwar jam’iyya sakamakon murabus da wasu su ka yi
  • An nada sababbin shugabanni na shiyyar Arewa, shugabar mata, sakataren walwala da gudanarwa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta maye guraben wadanda su ka bar majalisar NWC a sakamakon murabus ko samun matsayi a gwamnati.

Rahoton Daily Trust ya tabbatar da cewa a karshen zaman NWC da aka yi ranar Laraba a sakatariyar APC a Abuja, an sanar da canjin da aka samu.

Sakataren jam’iyya na kasa, Sanata Ajibola Bashiru ya ce an samu shugabannin ne ta hanyar zabe da aka gudanar domin a cigaba da tafiyar da NWC.

Dr. Abdullahi Umar Ganduje APC
Abdullahi Ganduje tare da Shugabannin APC Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

An maye gurbin Ministoci a APC

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da PDP Ta Dakatar Da Shugaban Matasa Saboda Ya Zargi Saraki

Mataimakin shugaban APC na shiyyar Arewa, Abubakar Kyari da Beta Edu wanda ta ke shugabar mata ta jam’iyya duk sun zama ministoci a gwamnati.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shi kuwa Salihu Muhammad Lukman ya yi murabus kamar yadda Murtala Yakubu Ajaka ya ajiye kujerarsa domin takarar gwamnan a jam’iyyar SDP.

Premium Times ta ce Hon Ali Bukar Dalori (Borno) ya zama sabon mataimakin shugaban APC na Arewa, shi ya hau kujerar da Sanata Kyari ya bari.

Hon. Garba Datti Muhammad (Kaduna) ya samu kujerar mataimakin shugaban jam’iyya na Arewa maso yamma da Sadiq Ango ya doke shi a zabe.

APC tayi sababbin sakatorori

Farfesa Abdul Karim Abubakar Kana (Nasarawa) shi ne sabon mai bada shawara a kan shari’a, da alama ya canji Ahmad El-Marzuq daga jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Ya Shiga Ganawar Sirri da Ribadu, Abdussalami kan Yakin ECOWAS a Nijar

Sauran wadanda aka zaba su ne: Hon. Donatus Nwankpa (Abia) a kujerar sakataren walwala, Mary Alile Idele (Edo) ta zama shugabar matan APC ta kasa.

Sabon mataimakin sakataren yada labarai shi ne Duro Meseko, sai sakataren gudanarwa na shiyya, Ikani Shuaibu Okolo, dukkansu biyun daga Kogi.

Hakan na zuwa ne bayan Dr Abdullahi Umar Ganduje da Ajibola Bashiru sun karbi ragamar jam’iyyar bayan taron NEC na 12 da aka yi kwanakin baya.

A zaman ne majalisar kolin ta ba NWC damar zakulo wadanda za su dare kan kujerun da su ka rage.

Asali: Legit.ng

Online view pixel