Shugaba a APC Ya Rubutawa Bola Tinubu Wasika, Ya ce ‘Ka Ba Mu Kunya’ a Mulki

Shugaba a APC Ya Rubutawa Bola Tinubu Wasika, Ya ce ‘Ka Ba Mu Kunya’ a Mulki

  • Salihu Mohammed Lukman ya aika budaddiyar wasika zuwa ga shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • Jagoran na jam’iyyar APC mai mulki ya na ganin ba gwamnatin tarayya ba ta fara da kafar dama ba
  • Bayan tsaida tikitin musulmi da musulmi a zaben 2023, Lukman yake cewa an musuluntar da NWC

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC, Salihu Mohammed Lukman ya rubuta budaddiyar wasika zuwa ga Bola Ahmed Tinubu.

Daily Trust ta rahoto Salihu Mohammed Lukman ya na cewa ba haka aka yi tsammani daga Bola Tinubu da ya hau mulki a Mayu ba.

Alhaji Salihu Mohammed Lukman ya fadawa Mai girma shugaban Najeriya cewa alamu sun fara nuna gwamnati mai-ci ta fara da kafar hagu.

Bola Tinubu
Bola Tinubu da wasu 'Yan APC Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Musulmi da Musulmi a NWC

A cewar ‘dan siyasar, majalisar gudanarwa watau NWC ta APC ta samu kan ta a irin yanayin da jam’iyyar ta shiga na tikitin musulmi da musulmi.

Kara karanta wannan

Wike zai sake gigita PDP, bayanai sun fito da ya hadu da Shugaban APC, Ganduje

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Goyon bayan Abdullahi Umar Ganduje da Ajibola Bashiru su ka samu daga shugaban kasar ya jawo shugabancin APC ya na hannun musulmai biyu.

Business Day ta ce Lukman ya ce zargin da ake yi wa jam’iyyar na maida kiristoci saniyar ware ya jawo rashin jituwa a APC da kuma cikin al'umma.

Baya ga haka, tsohon shugaban jam’iyyar ya ce Bola Tinubu ya ki kyale Umaru Tanko Al-Makura ko wani a Arewa ta tsakiya ya gaji Abdullahi Adamu.

Nadin Ministoci da Tinubu zai yi

A game da zaben Ministoci, Lukman ya na ganin gwamnatin Bola Tinubu ba ta dauko irin mutanen da za su taimaka mata wajen cin ma manufofinta ba.

"Abu na uku shi ne yanayin wadanda ka ke ba aiki. Mai girma, a duk lokacin kamfen zaben 2023, daga cikin abin tallata ka shi ne ka iya nemo kwararru.

Kara karanta wannan

Za ayi kuskure: Ƙusa a APC Ya Gargaɗi Tinubu a Kan Watsi da El-Rufai Wajen Naɗa Ministoci

Idan aka duba yadda ya dauke ka fiye da makonni takwas kafin ka zabo Ministocinka, an yi tunanin ka na daukar lokaci ne domin zakulo fitattun kwararru.
Amma duba da wadanda ka zabo, ka ba mafi yawan jam’iyya da kuma ‘yan Najeriya kunya.
A zahiri yake ga duk masu tunani siyasa ya sha gaban komai. A halin yanzu, burin da ‘yan jam’iyya da ‘yan Najeriya ke da shi a gwamnatinka ya rushe."

- Salihu Lukman

El-Rufai da kujerar Minista

Ku na da labarin yadda rahoton DSS ya jawo sha’awar sake zama Minista ya fita daga ran Malam Nasir El-Rufai duk da an tantace shi a majalisar dattawa.

Dama tun can tsohon Gwamnan ya nuna rokon shi Bola Tinubu ya yi domin su yi aiki tare, daga baya aka ce binciken tsaro ya hana a tafi da Malam El-Rufai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng