Mataimakin Kakakin Jam'iyyar APC na Kasa Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa, Ya Koma SDP

Mataimakin Kakakin Jam'iyyar APC na Kasa Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa, Ya Koma SDP

  • Babban jigon jam'iyyar APC a jihar Kogi kuma mataimakin kakakin jam'iyyar n aƙasa ya fice daga jam'iyyar
  • Murtala Yakubu Ajaka ya kuma yi murabus daga kan muƙaminsa na mamba a kwamitin gudanarwar jam'iyyar na ƙasa (NWC)
  • Ficewar Murtala daga jam'iyyar tana da alaƙa da burinsa na yin takarar gwamnan jihar a zaɓen watan Nuwamba da ke tafe

Jihar Kogi - Mataimakin kakakin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Hon. Murtala Yakubu Ajaka, ya yi murabus daga kan muƙaminsa a jam'iyyar.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa da ya aikewa shugaban jam'iyyar na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, cewar rahoton Leadership.

Mataimakin kakakin jam'iyyar APC na Kasa ya yi murabus
Murtala Ajaka ya fice daga jam'iyyar APC Hoto: Leadership.com
Asali: UGC

A cikin wasiƙar ya ce ya dalilin murabus ɗin sa ya biyo bayan daina zama mamban jam'iyyar da ya yi a mazaɓarsa ta Ajaka 1 cikin ƙaramar hukumar Igalamela/Odolu ta jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Batun Karbar N500m, Shugaban Tsagin Jam'iyyar Labour Party Ya Bayyana Gaskiya

Ya yabawa shugaban jam'iyyar na ƙasa kan nasarorin da jam'iyyar ta samu a ƙarƙashinsa, inda ya ce ya bar jam'iyyar ne kawai a ƙashin kansa sannan yana fatan su sake aiki tare a nan gaba, rahoton Tribune ya tabbatar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani ɓangare na wasiƙar na cewa:

"Na rubuto wannan wasiƙar ne domin na sanar da kai da sauran mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam'iyyar mu, matsayar da na yanke ta yin murabus daga muƙamina a matsayin mataimakin kakakin jam'iyya na ƙasa kuma mamba a NWC."
"Hakan ya biyo bayan daina zama ɗan jam'iyya da na yi, wanda tuni na sanar a rubuce ga shugaban jam'iyyar APC na mazaɓar Ajaka 1 cikin ƙaramar hukumar Igalamela/Odolu LGA ta jihar Kogi."

Zai yi takarar gwamna a ƙarƙashin jam'iyyar SDP

Kara karanta wannan

Rigima Sabuwa: Shugaban Tsagin Jam'iyyar Labour Party Ya Sha Da Kyar a Kotun Zabe, Bidiyon Ya Bayyana

Rahotanni sun tabbatar da fastocin Ajaka na takarar neman gwamnan jihar a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP), sun karaɗe ko ina a jihar Kogi, wanda hakan na nuna cewa ya fice daga jam'iyyar APC ne domin yin takara a zaɓen gwamnan jihar na watan Nuwamba mai zuwa.

Shugaba Ya Bayyana Abinda Zai Yi Bayan Ya Sauka Mulki

A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana babban abinda zai yi kewa, idan ya sauka daga kan mulkin ƙasar nan.

Shugaba Buhari ya ce mutanen da ke kusa da shi da suka yi aiki tare na tsawon shekara takwas, su ne zai yi kewa sosai bayan ya koma Daura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel