An Aike da Muhimmin Sako Mai Jan Hankali Ga Shugaba Tinubu Kan Shari'ar Zaben Gwamnan Kano

An Aike da Muhimmin Sako Mai Jan Hankali Ga Shugaba Tinubu Kan Shari'ar Zaben Gwamnan Kano

  • Wata kungiyar jama'a a Kano ta aika muhimmin sako ga shugaban kasa Bola Tinubu kan shari'ar zaben jihar
  • Kungiyar NWCSAC ta roki Tinubu a kan kada ya yarda ayi amfani da shi wajen murde sakamakon shari'ar da ake yi a kotun zaben jihar
  • Ana dai zargin wasu da kokarin bai wa alkalan kotun zaben jihar Kano cin hanci domin yin kutse a hukuncin da kotun zaben za ta yanke

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Wata kungiya mai yaki da rashawa a yankin Arewa maso yamma wato NWCSAC ta roki shugaban kasa Bola Tinubu da ya sanya baki a kan takkadamar da ke kewaye da gudanarwar kotun zabe a jihar Kano.

Kungiyar NWCSAC ta yi rokon ne a yayin da ta gudanar da zanga-zangar lumana a jihar Kano a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta, rahoton Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida Ya Karbi Matasan da Suka Fito Zanga-Zanga a Kano, Sabbin Bayanai Sun Fito

An nemi Tinubu ya shiga lamarin shari'ar zaben Kano
An Aike da Muhimmin Sako Mai Jan Hankali Ga Shugaba Tinubu Kan Shari'ar Zaben Gwamnan Kano Hoto: H.E Dr Nasir Yusuf Gawuna/Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Yunkurin murde sakamakon zaben Kano zai haifar da gagarumin tashin hankali

Jaridar Leadership ta rahoto cewa duk da gargadin da rundunar yan sandan jihar Kano ta yi, wasu mutane sun yi zanga-zanga kan zargin yunkuri da ake yi na ba wasu alkalan kotun zabe cin hanci a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta sanar da Tinubu cewa Kano da sauran jihohi sun riga sun shiga fargaba da tashin hankali a siyasance, don haka duk wani yunkuri na yin magudi a sakamakon zaben Kano na iya haifar da rikicin da ba a taba ganin irinsa ba wanda zai iya cinye kasar.

Jagoran kungiyar, Alhaji Ibrahim Waiya, a cikin wata wasika da ya gabatarwa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa kungiyar ta gudanar da zanga-zangar ne don sanar da shugaban kasa Tinubu abubuwan da ke fitowa daga kotun zabe a jihar a yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Jerin Jiga-Jigan Ministoci 9 da Zasu Fayyace Nasarar Shugaba Tinubu Ko Gazawa da Dalilai

Bukatar da kungiyar NWCSAC ta gabatarwa Tinubu

Waiya yi kira ga shugaban kasar da ya daraja girman damokradiyya ta hanyar nisantar duk wani abu da zai sa a yi amfani da shi wajen yin katsalandan a duk harkokin kotunan zabe, domin kare mutunci da kimarsa.

Kungiyar ta kunshi kungiyoyin dalibai, malamai, yan damokradiyya, da mutane masu kishin kasa a Kano da sauran jihohin arewa maso yamma guda shida, inda suke yaki da rashawa da rashin adalci, da kuma tallata yadda ake tafiyar da harkokin mulki.

Wani bangare na wasikar na cewa:

"Ya mai girma shugaban kasa, za ka tuna cewa a 2019, jihar Kano ta dauki zafi a kan abun da ake zargin taron dangi ne ta hanyar tasirin gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jam'iyyar APC a lokacin, da nufin yin magudi a sakamakon zaben da aka sake gudanarwa, kuma ta haka ne aka take yancin mutanen Kano na zabar shugabannin da suke muradi.

Kara karanta wannan

Shari'ar Zaɓen Jihar Kano: Rundunar 'Yan Sandan Ta Aike Da Muhimmin Sako Ga Masu Zanga-zanga

"Lamarin 'inconclusive' da aka yi ya riga ya shiga kundin tarihin siyasar Najeriya, a matsayin daya daga cikin lamura mafi muni a tarihin siyasar Najeriya.
"Manyan masu ruwa da tsaki a jihar sun yi kokari don hana barkewar rikici da aka shirya tayarwa sakamakon fusatar da al'umma suka yi, sai dai an kwantar da abun ta hanyar mika shi ga bangaren shari'a, hakan ya kara karfafa fatan da mutane ke yi na samun adalci daga bangaren shari'ar Najeriya.
"Ya mai girma shugaban kasa, duk da tashe-tashen hankular da aka samu a jihar Kano, a 2019 wanda muka shaida, an yi zargin cewa an sace kuri'un mutanen Kano da taimakon wasu hukumomi kamar na yan sanda, INEC da sauransu, kuma an ce hakan ya saba muradin mutanen Kano, duba ga sakamakon zaben.
"Hakazalika, 2023 ya sake zuwa, kuma alhakin kiyaye martabar kowane zabe a kasar nan ba wai ya rataya a wuyanka bane kawai, amma ya zama wajibi a addinance ka yi kokarin samar da yanayi mai kyau ga kowa.

Kara karanta wannan

Meye zai faru? Shugaban matasan PDP ya bayyana kwarin gwiwar tsige Tinubu a mulki

"Ya mai girma shugaban kasa, bayanan baya-bayan nan da aka alakanta da daya daga cikin alkalai a kotun zaben Kano, ya nuna karara cewa wasu mutane na aiki don yin murdiya a tsarin shari'a, duk da tarin damfarar zabe da aka tafka kamar su: magudi, amfani da kudi wajen siye masu kada kuri'u, yunkurin haifar da tashin hankali don tsorata masu zabe a Kano daga sauke hakkinsu na zabar dan takarar da suke ra'ayi.
"Matsayin wannan bayyani na tashin hankali da aka kirkira ta hanyar ayyukan wasu yan siyasa da idonsu ya rufe, ba wai kawai abin damuwa ba ne harma da hatsari ga ci gaba da dorewar dimokradiyyarmu. Mun yi imani cewa idan har aka bar wannan yanayin a tsarin dimokradiyyarmu, tare da bai wa wasu miyagun yan siyasa da ba su tunanin komai sai kansu damar cin galaba, sannu a hankali za a cinye mu.
"Idan har wata alkaliya ta kotun zabe za ta fito fili ta yi wannan tonon silili a bainar jama'a, tana mai korafi kan yadda ake ta kokarin ganin an juya matsayinta na son kamanta gaskiya, ya nuna lallai ba wannan bane karo na farko, kuma ta cancanci a yaba mata saboda wannan sadaukarwar da ta yi.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Dan Siyasa Da Wasu 2 a Wata Jihar Arewa

"Mun yi tunanin rubuta wannan wasikar ne domin mu gabatar maka da shi bayan wani zanga-zangar lumana da mutanen Kano suka yi wanda kungiyar NWCSAC ta shirya don nuna rashin jin dadinmu kan wannan yunkuri na bai wa alkalai cin hanci don murde sakamakon kararrakin zaben.
"Wannan jita-jita da ake yadawa don murde nasarar wasu zababbun shugabannin siyasa, ba wai hatsari ne da shi kawai ba, hakan kisan kai ne, wanda ka shafar martabar siyasarka, ba wai a Najeriya kawai ba harma a fadin kasashen duniya."

Jama'a sun gudanar da zanga-zanga a jihar Kano

A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu gungun mutane sun fara zanga-zangar lumana yanzu haka a kan titunan cikin birnin Kano duk da hukumar 'yan sanda ta haramta hakan, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kwamishinan rundunar yan sandan jihar Kano, Mohammed Usain Gumel, ya sanar da haramta duk wani nau'i na zanga-zanga a lungu da saƙo na jihar Kano bayan gano tuggun 'yan siyasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel