Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Dan Siyasa Da Wasu 2 a Kaduna

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Dan Siyasa Da Wasu 2 a Kaduna

  • Wasu tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da wani Kansila a anguwar Mai Taro da ke karamar hukumar Sabo ta jihar Kaduna
  • Maharan sun kuma sace wata mata tare da kansilan sannan suka kuma yi awon gaba da wani a unguwar Dankande
  • Sai dai zuwa yanzu rundunar yan sanda ko gwamnatin jihar bata tabbatar da harin da aka kai a ranar Asabar, 19 ga watan Agusta, ba a hukumance

Jihar Kaduna - Tsagerun yan bindiga da ake zaton masu fashi da makami ne sun yi awon gaba da kansilan gudunmar Garu da ke karamar hukumar Soba ta jihar Kaduna, Alhaji Sabitu Ahmad, da wasu mutane biyu.

An tattaro cewa maharan sun farmaki yankin Anguwar Mai Taro inda kansilan yake da zama sannan suka yi awon gaba da shi tare da wata mata a unguwar a ranar Asabar, 19 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Kama Karin Mutum 3 Cikin Wadanda Suka Yi Wa Sarkin Kano Ihun ‘Sabon Gwamna Sabon Sarki’

Yan bindiga sun sace kansila a jihar Kaduna
Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Dan Siyasa Da Wasu 2 a Kaduna Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Yan bindiga sun sace kakakin kansilolin karamar hukumar Soba ta jihar Kaduna

Jaridar Aminiya ta rahoto cewa, an kuma sace wani mutum guda a Unguwar Dankande da ke karamar hukumar ta Soba a ranar Juma'a, 18 ga watan Agusta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani mazaunin yankin mai suna Lawal Sani ya sanar da jaridar Aminiya cewa Kansilan da aka sace shine mai magana da yawun kansiloli a yankin.

Martanin rundunar yan sanda

Zuwa yanzu ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, ba domin baya amsa wayarsa kuma bai amsa sakon da aka tura masa ba.

Sai dai kuma, mai magana da yawun Gwamnar Jihar, Mohammmed Lawan Shehu ya ce har yanzu ba a sanar da shi lamarin ba a hukumance.

Kara karanta wannan

Yadda Matasa Suka Babbaka Wani Mai Satar Yara a Arewacin Najeriya, Sun Ceto Mata 2 Da Ya Sace

Yan bindiga sun sace fasto, sun kashe matarsa a jihar Edo

A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun harbe Misis Peace Chinyereugo, matar faston cocin Vineyard of Grace Dominion Assembly, Rev. Samuel Chinyereugo, a garin Benin, babban birnin jihar Edo.

Lamarin ya afku ne da misalin karfe 7:36 na yammacin ranar Litinin, 14 ga watan Agusta, a harabar cocin da ke lamba ta 101, Unguwar Upper Lawani, New Benin, garin Benin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel