Shari'ar Zabe: Rundunar 'Yan Sandan Kano Ta Haramta Duk Wani Nau'i Na Zanga-zanga a Fadin Jihar

Shari'ar Zabe: Rundunar 'Yan Sandan Kano Ta Haramta Duk Wani Nau'i Na Zanga-zanga a Fadin Jihar

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta haramta duk wata zanga-zanga da ake gudanarwa a fadin jihar
  • Hakan ya biyo bayan rahotannin da hukumar 'yan sandan ta samu na shirya zanga-zanga da manyan jam'iyyun jihar suka yi
  • Magoya bayan jam'iyyun APC da NNPP dai na gudanar da zanga-zanga kan hukuncin da kotun zaɓen jihar za ta yanke

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Rundunar 'yan sandan jihar Kano, ta haramta duk wani nau'i na zanga-zanga da ake gudanarwa dangane da hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓen jihar.

Rundunar ta tura jami'anta zuwa cikin gari domin dakatar da masu zanga-zangar kan hukuncin da kotun za ta yanke dangane da zaɓen gwamnan jihar Kano.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Mohammed Usaini Gumel ne ya bayyana hakan a hedikwatar hukumar a ranar Litinin kamar yadda jam'in hulɗa da jama'a na hukumar ya bayyana a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Jirgin Kaduna-Abuja: An Kama Manyan Mutane 2 da Ma'aikata Kan Shirin Yan Bindiga Na Sake Kai Hari

Rundunar 'yan sandan Kano ta haramta zanga-zanga a jihar.
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta haramta gudanar da zanga-zanga a faɗin jihar. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar 'yan sandan Kano ta dakatar da zanga-zangar da ake yi a jihar

Kwamishinan 'yan sandan ya bayyana cewa sun samu rahotanni kan zanga-zangar da magoya bayan manyan jam'iyyun jihar biyu suka shirya domin nuna adawa da hukuncin kotun za ta yanke a yau.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da alƙaliyar kotun zaɓen jihar Kano ta bayyanawa duniya cewa ana ƙoƙarin ba ta cin hanci domin sauya hukuncin kotun kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ta koka kan yadda wasu manyan 'yan siyasa suka tuntuɓeta da nufi su ba ta wani abu na cin hanci domin ta yanke hukuncin da zai yi mu su daɗi.

Kungiyoyi da dama musamman ma na fararen hula, sun yi Allah wadai da yadda wasu ke ƙoƙarin murƙushe dimokuraɗiyya.

Jam'iyyar APC ta zargi gwamnatin Kano da ba da cin hancin N10m

Kara karanta wannan

Kotun Zabe: Babban Malamin Addini Shawarci 'Yan Najeriya Kan Abin Da Za Su Yi Idan Kotun Koli Ta Yi Hukunci

A baya Legit.ng ta kawo muku rahoto kan zargin da jam'iyyar APC ta yi, na cewa gwamnatin jihar Kano ta jam'iyyar NNPP, na yunƙurin saye alƙalan da ke gudanar da shari'ar zaɓen jihar.

Jam'iyyar ta APC ta yi zargin cewa gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya yi yunkurin bai wa alƙalan da ke sauraron shari'ar cin hancin naira miliyan 10.

Jam'iyyar ta ƙara da cewa, gwamnatin jihar Kano mai ci ta ruɗe ne saboda hango faɗuwa ƙarara a shari'ar da ke gaban kotu.

Abba Gida Gida ya bemi a yi bincike kan ba da cin hanci a kotu

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan buƙatar da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya miƙa ga hukumomin yaƙi da cin hanci kan su bincika zarge-zargen bayar da cin hanci a kan shari'o'in jihar.

Abba ya bayyana hakan ne biyo bayan ƙorafin da alƙaliyar da ke sauraron shari'o'in jihar, Ngozi Azinge ta yi na cewa wasu manyan 'yan siyasa na yunƙurin bayar da cin hanci don karkatar da akalar shari'ar jihar.

Kara karanta wannan

Neman Alawus: Bidiyon Tubabbun Yan Boko Haram Suna Zanga-Zanga a Borno, Sun Rufe Hanya

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng