Abba Gida-Gida Ya Karbi Matasan da Suka Fito Zanga-Zanga a Kano, Sabbin Bayanai Sun Fito

Abba Gida-Gida Ya Karbi Matasan da Suka Fito Zanga-Zanga a Kano, Sabbin Bayanai Sun Fito

  • Matasa da suka gudanar da zanga-zanga kan shari'ar zaben gwamnan Kano sun je gidan gwamnati
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tarbi masu zanga-zanga a fadar gwamnati a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta
  • Matasan dai suna zargin shugaban jam'iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje na kokarin siye alkalan kotun zaben

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ya karbi bakuncin kungiyar matasa da suka gudanar da zanga-zangar lumana don neman adalci a kotun zaben gwamna.

Masu zanga-zangar, sun fito da yawansu dauke da kwalayen rubutu iri-irin don yin watsi da yunkurin da ake zargin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, yana yi kan shari'ar da ke gudana a kotun zabe, Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shari'ar Zaɓen Jihar Kano: Rundunar 'Yan Sandan Ta Aike Da Muhimmin Sako Ga Masu Zanga-zanga

Gwamnan jihar Kano ya karbi masu zanga-zanga a Kano
Abba Gida-Gida Ya Karbi Matasan da Suka Fito Zanga-Zanga a Kano, Sabbin Bayanai Sun Fito Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Matasa sun zargi Ganduje da yunkurin murde shari'ar zaben Kano

Channels TV ta rahoto cewa masu zanga-zangar sun yi zargin cewa, wata alkaliyar kotun zaben ta yi gargadi kan mutanen da ke kokarin bata cin hanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwalayen da masu zanga-zangar suka rike na dauke da rubutu kamar haka: "Gandola, ka daina sako rashawa a kotun zabe da ke gudana, Kano ta zabi Abba - Gida Gida, Mun shirya kare kuri'armu."

Wasu sun rubuta: "Ganduje kada ka murde sakamakon zaben, baka cancanci zama shugaban APC ba, ka barnata mana kudaden mu."

Jam'iyyun APC da NNPP sun kira mambobinsu don yin zanga-zanga a Kano

A tuna cewa rundunar yan sandan jihar Kano ta yi gargadi a kan gudanar da zanga-zanga kan sakamakon shari'ar da ke gudana a kotun zaben.

Jam'iyyar APC da jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar sun bayyana cewa sun yanke shawarar yin zanga-zanga a kan hukuncin kotun zaben.

Kara karanta wannan

To Fa: Sabuwar Zanga-Zanga Ta Ɓarke a Cikin Birnin Kano Duk da Umarnin Yan Sanda

NNPP ta tattara mambobinta daga fadin jihar a ranar Litinin don gudanar da gangami daga Kofar Nasarawa zuwa gidan gwamnati don zanga-zanga kan abun da suka kira da yunkurin kwace masu nasara da APC ke yi.

Ita kuma jam'iyyar adawa ta APC, ta bakin kakakinta, Ahmad Aruwa, ta fitar da wata sanarwa tana mai umurtan mambobinta da su fito kwansu da kwarkwata don tunkarar NNPP.

Hakan ne ya sa kwamishinan yan sandan jihar Kano, Muhammad Gumel, haramta duk wani nau'i na zanga-zanga a fadin jihar.

Fintiri ya taya Wike murnar zama minista

A wani labari na daban, mun ji cewa Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya taya tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, murna bisa muƙamin ministan birnin tarayya Abuja da a ka naɗa shi.

Wike yana daga cikin ministoci 45 da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta a babban ɗakin taro na fadar shugaban ƙasa, a birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng